Isra'ila ta ce ta ƙwace jirgin ruwan ƴan gwagwarmaya da ke son kai agaji Gaza

 Isra'ila ta ce ta ƙwace jirgin ruwan ƴan gwagwarmaya da ke son kai agaji Gaza



Isra'ila ta ce ta ƙwace jirgin ruwan ƴan gwagwarmaya da ke son kai agaji Gaza


Ma'aikatar harkokin wajen Isra'ila ta ce sojojin ƙasar sun karɓe ragamar wani jirgin ruwan ƴan gwagwarmaya yan sa-kai, da suka lashi takobin kangarewa haramcin Isra'ila, don kai agaji har zirin Gaza.

Wakiliyar BBC ta ce mutane goma sha biyu ne a cikin jirgin, kuma an musu bidiyon mintuna kaɗan kafin yanke sadarwarsu, an gansu sanye da rigunan ruwa, suna ihu, yayin da dakarun Isra'ilar ke daka masu tsawa suna neman su jefa wayoyinsu cikin ruwa.

An barbaɗa wa jirgin wani sinadari mai kama da hayaƙi don hana shi ganin gabansa kafin yi masa ƙawanya.

Za a kai su wata tashar jirgen ruwa ne da ke Isra'ila, daga nan a tasa keƴarsu zuwa gida.

Fasinjojin jirgin sun haɗa da ƴar gwagwarmayar yaƙi da matsalar sauyin yanayin nan yar Sweden Greta Thunberg, da wata ƴar majalisar tayayyar Turai ku

Post a Comment

أحدث أقدم