![]() |
Yadda Ake Magance Matsalar “Can’t Connect to the Camera” a Wayar Android (Cikakken Bayani 2025) |
Matsalar "Can't connect to the camera" na faruwa ne sau da yawa ga masu amfani da wayoyin Android. Wannan sakon yana bayyana ne idan wata manhaja ko wani abu na cikin wayar yana amfani da camera ko flashlight. A cikin wannan post, zan nuna maka matakai guda biyar da za su taimaka wajen gyara wannan matsala cikin sauki.
Ka matsa maɓallin Recent Apps ka rufe duk wata manhaja da ka buɗe, musamman WhatsApp, TikTok, ko Facebook. Bayan haka, ka ƙara buɗe camera.
Ka danna maɓallin wuta, sai ka zabi Restart. Wannan yana taimakawa wajen kawar da software bugs na ɗan lokaci.
Je zuwa Settings > Apps > Camera > Permissions, sannan ka tabbatar da cewa an ba da izini ga Camera da Microphone. Idan izinin bai kunnaba, camera ba za ta yi aiki ba.
Ka je Settings > Apps > Camera > Storage > Clear Cache. Idan matsalar ta ci gaba, ka gwada Clear Data amma ka lura zai goge wasu saitunan app ɗin.
Riƙe maɓallin wuta, sai ka zabi Reboot to Safe Mode. A wannan yanayin, wayarka ba za ta kunna dukkan apps na waje ba. Idan camera ta yi aiki, wata app ce ke haifar da matsalar. Ka goge apps da ka girka kwanan nan.
Matsalar “Can’t connect to the camera” ba ta da wahalar gyarawa idan ka bi waɗannan matakai. Ka tabbatar da cewa babu wata app da ke hana camera aiki, sannan kayi amfani da saituna cikin hikima. Idan kana buƙatar taimako kai tsaye, comment “GYARA” domin a turo maka PDF version.
can't connect to the camera, gyaran camera a Android, Android camera problem, fix Android camera error, app da ke hana camera aiki