Notification texts go here Contact Us Buy Now!

Bambanci tsakanin "Dr" na Likitanci, "Dr" na PhD, da kuma "Dr" na Honorary Degree?




Bambanci tsakanin "Dr" na Likitanci, "Dr" na PhD, da kuma "Dr" na Honorary Degree?

Na farko, Muna da "Dr" na Medical Doctor (Likita): Shi ne likitan asibiti, Ya yi karatu a fannin lafiya (Medicine & Surgery), ya kammala digiri irin su MBBS, Wannan Dr dinsa yana nufin shi likita ne mai duba mararsa lafiya da yi masu magani.

Misali: Dr. Aisha Musa, Likita a General Hospital.

Na biyu, "Dr" na PhD (Doctor of Philosophy, among others): Wannan ba likita bane a asibiti, illa dai malami ko mai bincike a jami’a, wanda ya fara da digiri na farko (BSc), sai ya yi Masters (Msc), daga baya kuma ya yi zurfin bincike har ya samu PhD, Wannan shi ne mafi girman digiri a jami’a, sai anyi karatu ake samu.

Misali: Dr. Aliyu Ibrahim PhD in Computer Science.

Na ukku, "Dr" na Honorary Doctorate Degree: Wannan kuma ba karatu akeyi ba, jami’a ce take bayar da digiri na girmamawa saboda gudummawar mutum a wani fanni. 

Ana kiran wanda aka girmama da wannan degree da (Dr) amma ba daidai yake da likita ko mai PhD ba.

Misali: (Dr) Dauda Kahutu Rarara an ba shi Honorary Doctorate Degree a bangaren da yafi kwarewa, saboda gudummawarsa ga ci gaban Al'ummarsa da kuma kwarewarsa. 

A takaice, Dr na Likita shine Medical Doctor da yake duba mu a asibiti, Dr na PhD shine mai bincike da kuma ilimi mai zurfi a jami’a, Dr na Honorary Degree ana bayarwa a matsayin girmamawa saboda gudummawa ga al’umma.

Saboda haka idan ka ji ana kiran mutum Dr, ka fahimci akwai bambanci tsakanin Dr na likita, Dr na karatu (PhD), da Dr na girmamawa (Honorary Degree).

Note: Abinda na fahimta da Rarara shi ba ruwan shi, nishadi ya mayar da abun, baya bari wani abu ya dame shi.

Allah yasa mu dace.

About the Author

Webmaster | Youtuber | Freelancer | Programmer | Sm Engineer | Blogger | Muslim | Sunni

Post a Comment

Cookie Consent
We serve cookies on this site to analyze traffic, remember your preferences, and optimize your experience.
Oops!
It seems there is something wrong with your internet connection. Please connect to the internet and start browsing again.
AdBlock Detected!
We have detected that you are using adblocking plugin in your browser.
The revenue we earn by the advertisements is used to manage this website, we request you to whitelist our website in your adblocking plugin.
Site is Blocked
Sorry! This site is not available in your country.