Maiyasa Manyan Project Ke Gudun Yan Nigeria
Zanyi amfani da KLOUT domin fada mana gaskiyane da bama son ji.
Klout sun dakatar da yan Nijeriya daga shiga project dinsu, saidai idan mutum yayi amfani da VPN. Dama tun jiya suka chire mutanen mu daga leaderboard, suka kwashewa yan Nijeriya points dinsu ya koma zero, da nayi musu magana sai suka ce suna wani gwaji ne amma zai dawo. Wani yayi comment a karkashin tweet dina jiya cewa klout sunyi wani tweet da sassafe da yake nuna cewa zasu chire yan Nijeriya amma chikin yan sakwanni suka goge tweet din, don haka da yawan mutane basu ga tweet din ba, daga baya kuma bayan sun kwashewa yan Nijeriya points dinsu sai sukayi posting cewa sun chire bots daga project dinsu, ma’ana dai yan Nijeriya ne bots din 😢. Sun kara tabbatar mini da hakan a safiyar nan, domin nayi musu magana akan cewa mai yasa sukayi blocking yan Nijeriya daga project dinsu? Sai suka amsa mini cewa basuyi blocking yan Nijeriya ba, amma sun dakatar da bots daga project dinsu.
Tunda naga project dinsu da sukayi backing din KLOUT wato Matheora nasha jinin jikina cewa za’a samu alkhairi dashi, daga baya naga mai Solana da kansa wato Yakovenko shine na daya akan leaderboard dinsu, na kara jin cewa tabbas wannan project dinsu da za’a samu alkhairi dashi, domin gaba daya Solana suna chikinsa tsamo-tsamo.
Projects sun fara gudun yan Nijeriya.
Idan zaku tuna kwanakin baya nayi rubutu akan wani abu daya yamutsa hazo a tweeter, wanda wasu manyan projects suka dinga yin tweet cewa duk project din da yake so yayi karko kada ya bari yan Nijeriya su shigeshi. Hujjarsu shine yan Nijeriya basa bawa projects gudummawa ta azo a gani, suna shiga project ne domin kawai suyi cashing out suyi gaba, sannan suna matsawa projects da pressure suyi launching koda basu shirya ba.
Ni aganina yin cashing out ba matsala bane, amma matsawa projects akan suyi launching babbar matsala ne. Duk projects na gaske suna da plan/roadmap da suke shiryawa na abubuwan da zasu chimma kafin suyi launching. Don haka suna bin wannan roadmap din nasu ne wajen building project dinsu, amma sai kaga mutanenmu suje suyi ta matsa musu da tambayar yaushe zasuyi launching? “When TGE” “When are you launching” da sauran tambayoyi marasa amfani da sawa projects pressure. Wani lokachin ma sai kaga ana fadawa project maganganu marasa amfani, kamar kiransu scammers, useless project, da sauransu. Wannan pressure ba iya yan Nijeriya bane kadai sukeyi harda yan Pakistan, India da sauransu amma yan Nijeriya mune kan gaba, domin a duk inda kaga mutane 10 suna yiwa project irin wayannan abubuwan zakaga 7 daga chiki yan Nijeriya ne.
Shawarar da zan bamu itace duk project da zamu shiga, idan har muka ga sun dade basuyi launching ba har mun gaji, to zaifi mana mu daina shi gaba daya, mu dauka hankalinmu daga kansa. Duk lokachin da mukaji labarin cewa zasuyi launching sai ayi damu, muyi cashing out na wahalar da mukayi musu a baya. Yau idan kana ganin ka gaji da minings da kake yi kamar HOT, Midas, CEX.IO da sauransu zaifi maka kanka watsar musu da abinsu kawai ka daina, ranar da kaji cewa zasuyi launching saika dawo ayi da kai.
Su kuma KLOUT zan kara magana dasu akan su bude yan Nijeriya, idan Allah yasa sun aminta shikenan, Idan kuma basu aminta ba sai mu bar musu kayansu su dauka sama!