Dalilin Da Ya Sa Salman Khan Bai Yi Aure Ba Har Yanzu – Labarin Soyayyarsa Da Yan Matan Bollywood
Shin Me Ya sa Har Yanzu Salman Khan Bai Yi Aure Ba?
Cikakken sunansa Abdurrashid Salim, sunan mahaifiyarsa Salma(shi yasa ake kiran sa da Salman Khan). An haife shi a ranar 27 ga Disamba 1965.
A tarihin Salman Khan ya yi soyayya da ƴan mata da yawa cikinsu akwai irinsu :
•Sangeeta Biljani
•Somy Ali
•Ashwarya Rai
.•Kafrina Muhammad Kaif. Da sauransu.
Amma a cikin su Ashwarya Rai ita ce wacce ya ƙarar da soyayyarsa akan ta. An haife ta a ranar 1 ga watan Nuwanba 1973. Aishwary Rai ta kasance kyakykyawar jaruma ajin ƙarshe a tarihin fina-finan India sannan ɗaya daga cikin matan da suka lashe kyautar sarauniyyar kyau ta duniya a shekarar 1994.
Tarihin Soyayyarsu
Soyayyarsu dai ta fara ne tun a loƙacin ɗaukar film ɗin babban mai bada umarnin nan wato 'Sanjay Leela Bansaley' wato HUM DIL DE CHUKE SANAM...
Da farko wannan soyayya ta fara gwanin ban sha'awa saboda yadda kowannensu ya ke ƙulafucin ɗan uwansa ta yadda ko ina za su je duk aikin da za ta je yana wurin haka kuma ita duk wani taro za a gan su a tare.
Haka dai wannan soyayya tayi ta tafiya har na tsawon shekaru biyu.
Kwatsam! A watan Maris na shekarar 2002 wannan soyayya ta zo ƙarshe inda ita Aishwary Rai da kanta ta fara gudun Salman Khan.
Jarumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne saboda jarumin ya fito ya yi iƙrarin cewa bada zuciya ɗaya ya ke zama da ita ba, saidai a na sa ɓangaren ya fito ya ƙaryata hakan a wancan loƙacin.
A wata hira da aka yi da jarumar ta furta cewa soyayya da tayi da shi ba ƙaramin matsala ta kawo a rayuwarta ba,amma ta godewa Allah da abin ya zo ƙarshe.
A yayin da wannan jaruma ke maganar sun rabu da juna, shi kuma a lokacin jarumin ya ke haukan son ta inda ya sha faɗa da mutane da dama akan ta musamman idan ya ga kana raɓar ta, kamar ya yi faɗa da Shah Rukh Khan wanda hakan ya kawo gaba a tsakaninsu ta tsawon shekaru amma a yanzu an sasanta.
Jaruma Aishwary ta bayyana cewa Salman Khan a wancan loƙacin da su ke soyayya ya sha dukanta akan yana zargin ta tana soyayya da wasu a masana'anta Bollywood, sannan
bayan rabuwarsu ya sha cin mutuncinta da na iyayenta.
A dalilin haka yasa har neman kariya ta kai wurin ƴan sanda,amma shi Salman Khan duk da haka bai daina son ta ba.....
Haƙiƙa jarumi Salman Khan yaso wannan baiwar Allah domin kuwa ya yi abubuwa da dama akanta domin an sha raɗe-raɗin a dalilinta bayan sun samu matsala ya je ya shawu har motarsa ta kwace har ya kashe wani.
A yayin da ita kuma Aishwarya Rai ta auri jarumi Abishek Amitabh Bachchan a shekarar 2017.