![]() |
Ranar Alƙiyama: Tsayuwar Shekaru Biliyan 18 Kafin Hisabi – Bayanai Dalla-Dalla |
18 billion years:
Day of Qiyama - Ina zaton mutane za su tsaya a filin Qiyama na tsawon shekaru biliyan goma sha takwas da miliyan Dari biyu da Hamsin (18,250,000,000) kafin a fara yin Hisabi wa mutane abubuwan da suka yi a lokacin da suka rayu a duniya.
هَذَا يَوْمٌ عَسِرٌ
____________________________
Ranar tashin Qiyama rana ce me girma da kowa yake dakon zuwan ta. Za ayi doguwar tsayuwar da ba a taɓa yin irin ta ba, wannan tsayuwar tana daga cikin dalilan da yasa aka kira ranar da ranar Qiyama (Ranar Tsayuwa), mutane maza da mata, Yara da manya, Musulmi da waɗanda ba su ba, za su tsaya a filin Mahshar na sama da tsawon shekaru biliyan goma sha takwas, a lissafin shekaru irin na duniya.
~ Manzon Allah (S.A.W) ya tabbatar da za a tsaya na tsawon shekaru dubu Hamsin (50,000 years, irin shekarun da Allah yake lissafi dasu) irin shekarun lahira.
~ A cikin Al-Qur'ani Allah ya bamu Ma'aunin da yake lissafin shekaru dashi, a wajen sa shekaru dubu ɗaya na duniya sune kwana ɗaya a lissafin wajen Ubangiji. Sai anyi shekaru dubu 'daya anan duniya Allah yake rubuta shi a matsayin kwana ɗaya a wajen Sa, hakan yana nuna mutane za su tsaya a gaban Ubangiji sama da shekaru biliyan 18.
~ A cikin Suratul Hajji, Surah ta 22, a Ayah ta 47, Allah yace:
وإن يوما عند ربك كألف سنة مما تعدون
Meaning:
“Tabbas, haƙiƙa kwana ɗaya a wajen Ubangijinka kamar shekaru dubu ne irin waɗanda kuke lissafawa (a nan duniya).”
~ Idan ka buga lissafi za ka ga cewa muna da kwanaki 365 a kowace shekara (at most), hakan yana nuna shekaru dubu ɗaya a wajenmu shi ne kwana ɗaya a wajen Allah, sai ka buga:
~ 1,000 × 365 = 365,000 years.
Wato sai mun shekara dubu 365,000 a nan duniya kafin Allah ya lissafa shekara ɗaya a wajenSa.
~ To sai kace 365,000 thousands years times 50,000 wato yawan shekarun da Bayi za suyi a tsaye a gaba Ubangiji irin shekarun lahira, ko a takaice:
365,000 × 50,000 = 18,250,000,000 yeears, irin na duniya.
~ Wannan tsayuwa ce kawai da mutane za suyi a gaban Allah, ba zaman gidan Aljannah ba ce da aka ce waɗanda suka shiga za su zauna har abada, shekarun tsayuwa da Hisabi ne kawai wannan.
~ Allah da kansa a cikin Surah ta 25 a Ayah ta 26 yace:
الملك يومئذ الحق للرحمن وكان يوما على الكافرين عسيرا
Meaning:
“Mulki a wannan ranar ya koma ga Allah Mai Rahama gaba ɗaya, wannan ranar za ta yi wahala wa kafirai.”
~ A cikin Suratul Qamar, Ayah ta 8 Allah yace:
مُهْطِعِينَ إِلَى الدَّاعِ يَقُولُ الْكَافِرُونَ هَذَا يَوْمٌ عَسِرٌ
Sai dai duk da waɗannan wahalhalun su Muminai ba za su ji azabar tsayuwar ba, Manzon Allah (S.A.W) yace:
~ “Na rantse da wanda raina yake a hannunsa (Allah kenan) za a sassauta wa Muminai wannan ranar, za su ga tsayuwar kamar ba ta wuce kamar mutum ya yi Sallar Farilla ya sallame ba.”
~ Wato Muminai ba za su ji wahalar tsayuwar shekaru Biliyan 18 ɗin nan ba, za su ga kamar sun tsaya ne na tazarar da ba ta wuce ka yi sallah ka yi sallama ba ko ƙasa da haka.
والذي نفسي بيده إنه ليخفف على المؤمن حتى يكون عليه أخف من صلاة مكتوبة
~ Wato mafi tsanani dai Muminai za su ga kamar minti 15 suka yi a tsaye, yayin da kafirai za su ga sun shafe shekaru Biliyan 18 a wajen.
A cikin "Al-Mustadrak" na Imamul Hakim, Manzon Allah yace:
"Tsawon ranar Qiyama a wajen Muminai bai wuce kamar tazara ko (interval) ɗin dake tsakanin Sallar azahar da La'asar ba.”
~ Sheikh Muhammad Nasir yace wannan Hadisin Sahihi ne (8,193)....
يوم القيامة على المؤمنين كقدر ما بين الظهر والعصر
~ A wannan Hadisin, Allah zai sassauta wa Muminai za su ga kamar tsayuwar awanni biyu ko biyu da rabi kawai suka yi.
Amma a zahiri 50,000 thousands years irin na lahira suka yi, wato 18 Billion 250 million years.
~ Allah ya sanya mu cikin waɗanda za a sassauta musu wannan tsayuwar.
Tsayuwa ko na awanni 18 ne ba ƙaramin tashin hankali ne ba, balle shekaru Biliyan 18 har ma da shekaru Miliyan 250.
Allah yace game da ranar tsayuwar, masu laifi da tauye mudu, da sabon Allah:
أَلَا يَظُنُّ أُولَئِكَ أَنَّهُمْ مَبْعُوثُونَ لِيَوْمٍ عَظِيمٍ يَوْمَ يَقُومُ النَّاسُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ
~ Cosmologists sun ce sun fahimci yanzu haka duniya ta kai shekaru Biliyan 17 zuwa 18 da halittar ta.
Nan gaba idan anje lahira za ayi tsayuwar da ya wuce shekarun da duniya ta yi a halicce, wannan duk ba a zo maganar shekarun da za a yi a Aljannah ko wuta ba da aka ce har abada.
~ Dukkan Aiyukan da muke yi, Sallah, Azumi da sauran su sune aiyukan da idan an karɓe su acikin records ɗin mu za a sassauta mana wannan doguwar tsayuwar.
~ Manyan abubuwan tsoro a wannan tsayuwar guda hudu ne:
1. Babu zama sai tsayuwa a kan babbar yatsar ƙafa guda ɗaya.
2. Babu cin abinci babu shan ruwa.
3. Babu inda mutum zai taka ya je balle ya motsa ƙafar.
4. Sannan babu wanda yasan ina zai je idan an zo an yi Hisabin, wuta ko Aljannah...
~ Duk duniya babu wanda zai iya roƙon Allah ayi haƙuri a sassauta wannan tsayuwar sai Manzon Allah (S.A.W), mutane za su je wajen Annabi Adam, zai ce ba zan iya ba, sai a dunguma aje wajen Annabi Nuhu, Ibrahim, Musa da Isah (A.S) duk ba za su iya ba, sai Muhammad Bin Abdullah (S.A.W)...
~ Ya Allah ka yafe mu, ka sassauta mana a nan duniya da kuma wancan rana ta Hisabi.
Allah kayi mana Alfarma mu samu kanmu cikin waɗanda za a sassauta musu wannan Azaba.
✍️:
Repost:
April — 10th, 2023.