Wannan "Stars intermediate challenge" da kake gani a Professional dashboard na Facebook, wani bangare ne na tsarin Facebook Stars, wanda ke baiwa content Creator damar samun kuɗi ta hanyar karɓar Stars daga masoyan su yayin da suke kallon bidiyon su na live ,reel ko stream.
Ga yadda yake aiki:
Stars Challenge na Sati ne ko wata-wata.
Facebook na saka wani (task) da za ka ci, kamar:
Yin live streaming har sau wani adadi cikin sati.
Samun yawan viewers ko engagements.
Received na wani adadin Stars daga masu kallo.
Idan ka kammala kashi 100% na wannan challenge, zaka samu badge na musamman da kuma karin opportunity a tsarin samun kuɗin Stars.
A wannan challenge din ana bukatar wani yatura Maka ⭐ Star sannan Kuma ka kammala post guda biyar kamar yadda suka bukata se Kuma costomize na star message.