Yadda Sheikh Kabiru Ya Warware Maganganun Dr. Umar Kani Cikin Ladabi Da Hujoji

Sheikh Kabiru ya yi raddi cikin ladabi ga Dr. Umar Kani, inda ya warware fahimtar da ba ta da tushe game da soyayyar Manzon Allah (S.A.W). An tattauna

 Yadda Sheikh Kabiru Ya Warware Maganganun Dr. Umar Kani Cikin Ladabi Da Hujoji



Yadda Sheikh Kabiru Ya Warware Maganganun Dr. Umar Kani Cikin Ladabi Da Hujoji
Sheikh Kabiru Ya Warware Maganganun Dr. Umar Kani Cikin Ladabi Da Hujoji


Sheikh Kabiru da Dr. Umar Kani 

Sheikh Kabiru ya yi raddinsa cikin ladabi tare da rushe dukkan fahimtar Dr. Kani da ya kawo maras tushe. Wallahi ban taba jin raddi mai tsafta, gishiri da borkono cikin ruwan sanyi irin wannan ba. Mallam Izala/Salafiyya suna da matasa fitinannu a ilimin hadisi da littafi. 

Wannan ya sa nima nake jan hankali cikin ruwan sanyi ga matasan dariku masu makauniyar biyayya. Gaskiya daya ce, hadisin da Triumph yake magana a kansa bai ganta ba ta kowacce fuska. Amma tun da har kun mayar da abin siyasa da sunan soyayar Manzon Allah (s.a.w) to yanzu kam sai ku yi ta kanku. 

Kagaggun karamomi ne aka yabawa Manzon Allah (s.a.w) dan a daga darajarsa. Shi kuma annabi ba a masa karya, duk wanda ya masa ya tanadi gidansa a wuta. Soyayyar annabi ba hauka ba ce; hankali ce da kowanne musulmi ya kamata ya san iyakokinsa. 

Annabi yana da daraja, kuma kyau da tsarin rayuwarsa ne ya sa ake koyi da shi, amma ba dan ya kasance shi mutum ba. Imani da shi wahayi ne. Allah ne ya zabe shi saboda ya fi kowa cikar kamala, matsayi da kuma biyayya. Ka dauki annabi ka kaishi wajen Allah kuskure ne. Ka shiga rigar son annabi da jahilci ko da sharri kuskure ne. Ka rika tara suma da datti ba gyara bakinka yana wari iskanci ne. Duk abin da ya shafi annabi tsaftacecce ne; na daga ilimi da komai. 

Musulman Dubai, Kuwait, Bahrain, Masar, Qatar, Saudia, Malaysia, India da Pakistan da sauran kasashe ba haka suke addini da sunan son Manzon Allah (s.a.w). Ka kalle su ka ga kanka, shin haka ne musulunci a wajenka? Da an fada maka gaskiya sai ka danna ashar, ko ka koma gefe ka hada kai dan yan uwanka yan bid’a kana cewa ba a son annabi. Ya kamata mu gane ba wani musulmi da ba ya son annabi, idan ka ga yana shirme tun asali ba a dora shi akan ilimi mai tsafta bane. 

Saboda haka Izala ko Wahabiyya ba su ne matsalar musulmi a Arewa ba, karatu ne matsalar mutanenmu da kin karbar gaskiya saboda malamai suna cin amanar ilimi wajen da’awa. Su Izala su yi ta munana lafazi dan ba a fahimci gaskiya ba, su kuma yan darika su yi ta danno ashar suna cewa makiya annabi. Yanzu fisabilillahi da Sheikh Kabiru bai fito ya warware malamin nan ba da shikenan jahilai daga cikin yan Tijjaniya da darika sun yarda da shi. 

Ko da yake ba laifinsa bane, wannan shi ne illar duk wanda mu ka ga Dr. a gaban sunansa sai mu dauka ya fi kowa ilimi. Bayan kuma wannan din kansa karancin ilimi ke kawo shi. Idan ni dan Arewa ne mai neman gaskiya a littafi ba zan sake irin su Sheikh Yahaya Haifan, Dr. Bashir, Dr. Birnin Kudu, Mallam Alkasim Hotoro da irin su Guruntum ba, kai ka san ko banza suna da adalci. Kai hatta irin su farfesa Maqari kai kasan suna da adalci, idan ban da kokarinsu na dole sai nassi ya yi daidai da akidarsu ba. 

To haka wannan matashi da ake wa lakabi da hayaki fidda na kogo. Daman shi ya matsawa Abduljabbar har ya kora shi gidan kurkuku. A irin wannan masifar tasa ta taksisin nassi waye zai sha a hannunsa idan mutum ya feso karya a Manzon Allah (s.a.w). Mai laya ya kiyayi mai zamani. Ku bar yan kungiya su yi ci da addininsu, amma maganar nassi da inganci ku bar musu. Ilimin addini da dalilin yin addini a barwa Ahlussuna.

About the author

Nuhu Saad Kumurya
Webmaster | Youtuber | Freelancer | Programmer | Sm Engineer | Blogger | Muslim | Sunni

Post a Comment