Tinubu Ya Tilasta Bin Dokar NERD Kafin Rajistar NYSC: Sabon Sharadi Ga Duk Ɗaliban Najeriya Daga Oktoba 6
![]() |
Photo: nannews.ng |
Shugaba Bola Tinubu ya amince da tilasta bin Dokar Ƙasa ta Nigeria Education Repository and Databank (NERD) a matsayin sharadi na dole kafin a yi wa ɗalibai rajista ko a basu takardar keɓewa daga shirin NYSC.
Wannan mataki zai fara aiki ne daga ranar 6 ga Oktoba, kuma daga wannan lokaci babu wani ɗalibi ɗan Najeriya – ko ya kammala karatu a jami’a ce ta gida, ko a kwalejin ilimi, ko a wata cibiyar ƙasashen waje – da za a iya yi wa rajista ko keɓewa daga NYSC ba tare da ya nuna shaidar bin ka’idar NERD ba.
Wannan umarni na ƙunshe ne cikin wata takarda da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya aika ga dukkan Ma’aikatun Tarayya, Hukumomi da Sassan Gwamnati (MDAs) a ranar Lahadi a birnin Abuja.
An bayyana cewa wannan sabon tsarin ba zai shafi masu aikin NYSC da suka riga suka shiga shirin kafin ranar fara aiwatar da dokar ba.
Akume ya ce umarnin yana da nufin aiwatar da shawarar Shugaba Tinubu kan sabunta tsarin rajistar NYSC, ta yadda za a tabbatar cewa duk wanda zai shiga ko ya keɓe daga shirin NYSC ya bi ka’idar NERD, komai inda ya kammala karatu.
Daya daga cikin muhimman buƙatu na wannan sabon tsarin shi ne dalibai su ajiye takardun aikin kammalawarsu, kamar thesis ko project report, a ma’ajiyar NERD.
An yi wannan tsarin ne domin ya zama hanyar tabbatar da ingancin ilimi, da tabbatar da cewa kowanne ɗalibi yana da hujjar shigarsa da ci gaba da karatu a kowanne lokaci. Haka kuma yana taimakawa wajen auna aikin karatu da bin diddigin bayanai, ba tare da la’akari da inda ɗalibin yake ba.
A watan Maris 2025, Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya bayyana karin bayani yayin da aka sanar da fara aiki da dokar NERD. Ya ce, bisa ga tanade-tanaden dokar NERD, kowane ɗalibi dole ne ya miƙa takardun aikinsa kamar yadda aka fayyace a sashe-sashe na dokar, ciki har da 2.3, 4.3(1), da 7.6.11(c).
Dokar NERD tana aiki ne ga dukkan cibiyoyin ilimi ba tare da la’akari da nau’in mallaka ba, ko na gwamnati ne ko na masu zaman kansu, soja ko farar hula, ciki har da makarantu na aikin jinya, noma, cibiyoyin bincike, da sauran cibiyoyin musamman.
Shugaba Tinubu ya kuma amince da tsarin biyan lada da samun kuɗi daga ajiye takardun ilimi domin dalibai da malamansu su rika samun kuɗi har tsawon lokaci daga abubuwan da suka ajiye.
An karfafa cibiyoyin ilimi su kafa ma’ajiyar bayanai ta cikin gida, domin inganta hadin gwiwa tsakanin jami’o’i da cibiyoyi da ke aiki ba tare da tsari na haɗin kai ba a baya.
Gwamnatin Tarayya ta kuma umurci dukkan cibiyoyi da hukumomi da su fara cikakken aiwatar da NERD. Hukumar NIMC da sauran hukumomin bayanai za su bayar da haɗin kai ta hanyar API domin tabbatar da sauƙin haɗawa da tantance bayanai.
Mai magana da yawun NERD, Haula Galadima, ta bayyana cewa kowace takarda da ɗalibi zai ajiye a tsarin za ta ƙunshi cikakken sunan ɗalibi, sunan mai kula da shi, ko akwai mataimaki, da na shugaban sashen karatu, tare da sunan jami’a da sashen da ya fito.
Galadima ta ce manufar shirin ita ce ta ƙara inganci da gaskiya a tsarin karatun Najeriya. Idan malamai sun san cewa sunansu zai bayyana a dandalin dijital na ƙasa da duniya ke iya gani, za su kula sosai wajen tabbatar da cewa takardun ɗalibansu sun cika ka’idoji.
Ta ƙara da cewa, da wuya wani malami ya so a danganta sunansa da aikin da bai da inganci. Wannan tsarin zai kuma taimaka wajen tabbatar da cewa malamai suna samun hakkinsu na alawus ta hanyar ingantaccen kulawa da aikin ɗalibai.
An bayyana cewa cibiyoyin gwamnati, jami’o’i, da kamfanoni za su iya yin rajista ta hanyar: