Notification texts go here Contact Us Buy Now!

Hadin Gwiwar Malamai da Ƴan Bindiga: Abinda Ziyarar Shaikh Asadussunnah ga Bello Turji ke Nuna Mana a Najeriya


Hadin Gwiwar Malamai da Ƴan Bindiga: Abinda Ziyarar Shaikh Asadussunnah ga Bello Turji ke Nuna Mana a Najeriya




🚨 Abubuwan da na fahimta bayan sauraron Sh. Asadussunnah akan haduwarsu da Bello Turji.

A cewarsa (Shaikh), last month alone, sun je wajen Bello Turji sau uku, sun samu ganawa da shi. Sannan a wannan watan da muke ciki, shima sun sake komawa. Me wannan yake nuna mana?

1. Gobnati ba da gaske take ba akan kama Turji. Idan har za'a iya zuwa a gana da shi, ya kamata Nigerian government tayi amfani da wannan Nicomsat 2 satellites 🛰️ din da suka kashe billions of naira from our tax to find Turji. Kai asa ba satellite din bata yi, to Nigeria tana da drones, ayi amfani da stealth drones abi su Shaikh har inda Turji yake. Kai idan ma babu, ayi amfani da UN or AU task force na hadin gwuiwa suyi proving tech support mana. 

2. Shaikh yace akwai wasu yan bindiga da sojoji suka ce sun kashe. Har suka rika saka hotunansu suna murna wai sunyi nasara. Sai ga mutane a raye. Ba su mutu ba. Wannan me yake nuna mana? Yana nuna mana cewa Nigerian Intelligence community basu da accurate Intel akan targets dinsu. Kawai bulayi suke a cikin duhu. Zasu iya kama wrong target, zasu iya kashe wrong target, zasu iya sakin target. Though i m not surprised. Ko kama Sultan ya isa ya tabbatar maka da cewa babu accurate Intel a wajen jami'an kasarnan.

To, duk wanda aka kashe daga lokacin da aka fara gwagwarmayar nan, da wanda aka jikkata, Allah ya saka musu. Tayar mana da hankula da ake akan tsaro Allah ya isa. Kuma a daina zuwa ana raina mana hankali. It is crystal clear rhat government has no plan for Turji, kuma they are not ready to handle this crisis. Ni Wallahi sojoji nake tausayi. Kusan duk sati biyu ko uku sai an kashe bayin ALLAH. Kuma a banza. Za'a iya kama Turji ba tare da ko mutum daya ya mutu ba.

Allah yana kallo. Kuma duk wanda yace wannan maganar siyasa ce Allah ya tsine wa makaryaci.

About the Author

Webmaster | Youtuber | Freelancer | Programmer | Sm Engineer | Blogger | Muslim | Sunni

Post a Comment

Cookie Consent
We serve cookies on this site to analyze traffic, remember your preferences, and optimize your experience.
Oops!
It seems there is something wrong with your internet connection. Please connect to the internet and start browsing again.
AdBlock Detected!
We have detected that you are using adblocking plugin in your browser.
The revenue we earn by the advertisements is used to manage this website, we request you to whitelist our website in your adblocking plugin.
Site is Blocked
Sorry! This site is not available in your country.