Yadda Ake Fara Kasuwanci da Naira 10,000 a Najeriya (Mataki-mataki)

Koyi yadda ake fara kasuwanci da N10,000 a Najeriya. Wannan cikakken jagora zai koya maka sana’o’i masu sauki, yadda zaka raba jarin ka, da matakai do

 

Yadda Ake Fara Kasuwanci da Naira 10,000 a Najeriya (Mataki-mataki)




Yadda Ake Fara Kasuwanci da Naira 10,000 a Najeriya (Mataki-mataki)

Yadda Ake Fara Kasuwanci da Naira 10,000 a Najeriya (Mataki-mataki)


Koyi yadda ake fara kasuwanci da N10,000 a Najeriya. Wannan cikakken jagora zai koya maka sana’o’i masu sauki, yadda zaka raba jarin ka, da matakai don samun riba.





Kasuwanci ba sai da miliyoyi ake fara shi ba. 

Duk wanda ke da azama da ilimi, zai iya fara sana’a da dan karamin jari kamar N10,000. A wannan jagorar, zan nuna maka yadda zaka zabi kasuwanci, yanda zaka raba kudin ka, hanyoyin tallatawa da matakin cigaba.





1. Fahimtar Abubuwan Da Zaka Iya Yi da N10,000


Idan kana da N10,000, abu na farko da zaka fara tunani akai shine "Menene zan iya yi da wannan?" Ga wasu sana’o’i da kake iya farawa da wannan adadi:


Sayar da ruwa da lemo a gaban gida ko kasuwa


Masa da Wake business a safe


POS agent (idan kana da katin ID da location mai kyau)


Sayar da sabulun wanka da gyaran jiki


Kananan kayan kwalliya (lip gloss, eye pencil, turare)


Siyar da snacks a makarantu


Zanen henna ko gyaran gashi a gida



Kowanne daga cikin waɗannan na iya fara da jari na N5,000 zuwa N10,000.



2. Yadda Zaka Tsara Jarin N10,000


Ga Misalin Tsarin Kudin POS Business:



Shawara: Ka tabbata koda N10,000 kake dashi, zaka iya ware ƙaramin kaso domin tallatawa da juya jari.





3. Hanyoyin Tallata Kasuwancin Ka da Karamin Kudi


Tallata kasuwanci yana da matukar muhimmanci, musamman a wannan zamani.


 1. WhatsApp Status:

Rika saka hoton kayan da kake siyarwa tare da farashi da lambar waya.


2. Facebook Personal Account da Groups:

Rubuta post mai jan hankali, saka hoton kaya, da kiran kai tsaye ("DM don oda")


3. Bayan Sallah & Gida:

Yi amfani da baki – makwabta, masallatai, ko abokan aiki. Ka bude baki, ka sanar da mutane.


Misali na Status Caption:


“Masa da wake masu dumi a safiya! Farashi mai rahusa. Ana kawo su har gida. DM ko kira 070xxxxxx.”







 4. Yadda Ake Kara Girman Kasuwancin Ka Cikin Watanni


Kasuwanci yana girma ne da:


Rikon gaskiya da amana


Bunkasa abokan ciniki (repeat customers)


Ajiye kason riba don kara jari


Gwamnati ko NGOs – suna bayar da tallafi ga kananan sana’o’i.


Zama mai saurin koyon dabaru daga YouTube, blogs da sauransu.



 Abin Da Zaka Kula Da Shi:


Kada ka dauki bashin da zai ruguza ka


Kada ka sayi kaya fiye da bukata


Ka nemi shawara daga wanda ya riga ka




5. Shawara Ga Matasa da Mata


Wannan jagora yana da matukar amfani ga:


Daliban da ke neman jari bayan makaranta


Matasa masu son rage zaman banza


Mata masu gida da ke son samun kudin kai


Kowane mai burin cin gashin kansa



 Kar ka jira sai ka tara miliyoyi kafin ka fara. Ka fara yanzu. Ka tashi daga inda kake.





Karamin jari kamar N10,000 na iya zama ginshikin gobe mai kyau. Idan ka tsara, ka dage, ka rike gaskiya – zaka iya zama attajiri mai suna. Fara yau, kar ka jira sai gobe.


Ka shirya? Ka zabi sana’ar da ta fi dacewa da kai ka fara mataki na farko yau.

 

About the author

Nuhu Saad Kumurya
Webmaster | Youtuber | Freelancer | Programmer | Sm Engineer | Blogger | Muslim | Sunni

Post a Comment