Matar da ke fuskantar rashin kulawa a aure tana cikin damuwa
Dalilan Da Ke Jefa Wasu Mata Cikin Soyayya Da Mata: Matsalolin Aure Ko Rashin Fahimta?
A zamanin nan, muna jin labarai da yawa game da wasu mata da ke komawa soyayya da mata (lesbianism). A wasu lokuta, ba wai saboda sha’awa bane, sai dai saboda wasu matsaloli da suka taso a cikin rayuwar aure – musamman rashin kulawa daga miji.
Wata Baiwar Allah Ta Bayyana:
A wata tattaunawa da wata mata, ta bayyana cewa dalilin da ya jefa ta cikin wannan hali shi ne rashin gamsuwa a aure. Tace:
> "Ni macece da nake buƙatar miji ya kula dani sosai yayin mu'amala. Duk da tsaftata da ƙoƙarina, mijina baya yi min wasanni ko gamsarwa. Na roƙe shi ya dinga gamsar da ni ta hanya mai kyau, amma yace shi ko yau aka haifi mace, ba zai iya hakan ba."
A cikin wannan halin na damuwa, wata ƙawarta ta fara nuna mata kulawa, har hakan ya juye zuwa soyayya da mu’amala tsakaninsu. Daga nan, sai ta fara jin cewa mace ta fi iya fahimtar mace fiye da namiji.
Abin Da Ya Kamata Maza Su Gane:
Wasu maza suna jin cewa wasanni ko tsotsar jiki lokacin mu’amala abin kyama ne. Amma gaskiyar ita ce, wannan na daga cikin hanyoyin da ake gina soyayya da nishadi a aure. Rashin fahimtar bukatun mace na iya jefa aure cikin barazana, ko kuma janyo ita mace ta fara duba wata hanya daban don samun gamsuwa.
Me Mata Ke Bukata a Aure?
Fahimta da sauraro
Gamsuwa a halal
Tattaunawa akan soyayya
Tsafta da kulawa
Aure ba kawai saduwa ba ne – yana buƙatar lokaci, fahimta da kuma juna biyayya. Lokacin da mace ta rasa waɗannan abubuwa daga mijinta, tana iya fara jin cewa wani (ko wata) na waje ne zai iya ba ta.
Karin Shawara Ga Maza:
1. Ku rika tattaunawa da matanku ba tare da kyama ba.
2. Ku fahimci bukatun su a cikin halal.
3. Ku dauki kulawa a matsayin sadaka da ibada.
4. Ku guji nuna cewa jima’i ko wasanni a jiki abu ne na ɓata tarbiyya – domin yana gyara aure ne, ba cutarwa ba.
Kuma Mata Ku Tashi Ku Kare Kanku:
Soyayya tsakanin mace da mace ba mafita bace. Ki bayyana bukatarki cikin hikima da tsafta. Ki fahimci cewa aure da namiji halal ne, kuma sai da ƙoƙari da kulawa ne yake bunƙasa.
Kammalawa:
Abin da ke jefa wasu mata cikin irin wannan hali shine rashin kulawa da gamsuwa daga mazajensu. Idan ma’aurata sun fahimci juna, suka tsaftace zuciya da jikinsu, aure zai zama mafita ba matsala ba.
Aure kulawa ne, ba kawai jima’i ba. Fahimta garkuwa ce, kulawa kariya ce.
Daga: Nuhu Saad Kumurya
Kumurya Media Inc.