Yadda Ake Mayar da Windows Idan Ya Lalace (System Restore)
Kwamfuta tana aiki ne bisa tsarin da ke haɗa software da hardware. Idan ɗaya daga cikin waɗannan ya lalace ko ya sami tangarda, tsarin Windows zai iya daina aiki yadda ya kamata. Matsalolin na iya kasancewa saboda shigar da sabbin software marasa inganci, sabunta Windows (update) da ta kawo matsala, cutar virus, ko kuskuren mai amfani wajen canza tsarin registry. A irin wannan yanayi, mutane da dama sukan ɗauki matakin sake shigar da Windows gaba ɗaya, alhali akwai hanyar da ta fi sauƙi da sauri wato System Restore.
System Restore wata hanya ce da ke ba ka damar mayar da tsarin kwamfutarka zuwa wani lokaci da tana aiki lafiya. Tsarin yana amfani da abin da ake kira Restore Points, wato wasu ajiyoyin tsarin da Windows ke yi ta atomatik ko da hannu. Wannan hanyar ba ta goge fayilolinka na sirri kamar hotuna ko takardu ba. Abin da take yi shi ne mayar da tsarin cikin yanayin da yake kafin matsalar ta faru.
Alamun Lalacewar Windows
Kafin ka yanke shawarar amfani da System Restore, yana da muhimmanci ka fahimci alamun da ke nuna tsarin Windows ɗinka ya lalace ko yana buƙatar mayarwa baya. Ga wasu daga cikin manyan alamun:
Kwamfutar ka tana jinkiri sosai wajen buɗewa da aiki.
Akwai kurakurai marasa dalili lokacin amfani da apps ko Windows.
Bayan (update), matsala ta bayyana nan da nan.
Wasu sassa na tsarin Windows sun daina aiki kamar yadda ya kamata.
Blue Screen (BSOD) tana bayyana akai-akai.
Kwamfuta tana sake kunna kanta kai tsaye ba tare da gargadi ba.
Windows bai buɗe gaba ɗaya ba ko yana makalewa a allon loading.
Idan ɗaya daga cikin waɗannan alamomi ya bayyana, System Restore na iya zama hanyar da za ta dawo da tsarin cikin yanayi mai kyau ba tare da shigar da Windows daga farko ba.
Menene System Restore?
System Restore wata hanya ce ta dawo da tsarin Windows zuwa wani lokaci a baya lokacin da komai ke aiki daidai. Windows yana ƙirƙirar restore points ta atomatik kafin manyan abubuwa su faru, kamar sabuntawa, shigar da software, ko canje-canje a tsarin. Za ka iya kuma ƙirƙirar restore point da kanka idan kana son ka tabbatar da kariya kafin ka yi wani abu mai muhimmanci.
Abin da System Restore ke dawo da shi ya haɗa da:
Saitunan tsarin (System settings)
Shigarwar registry
Fayilolin tsarin Windows
Manyan fayilolin tsarin da ke da alaƙa da drivers da software
Abin da baya dawo da shi:
Takardu, hotuna, bidiyo, da sauran fayilolin sirri
Software da ka shigar bayan ranar restore point
Sabbin updates da aka saka bayan restore point
Saboda haka, amfani da System Restore ba zai goge bayananka ba, amma zai iya cire software ko updates da suka kawo matsala.
Matakai na Amfani da System Restore a Windows 10
1. Buɗe Control Panel: Danna maɓallin “Start”, rubuta Control Panel sannan ka buɗe.
2. Je zuwa System and Security: Zaɓi “System” daga jerin.
3. A gefen hagu, danna “System Protection”.
4. Zai buɗe taga mai suna “System Properties”. A nan, danna “System Restore”.
5. Zaɓi “Next” domin ganin jerin restore points da tsarin ya ƙirƙira.
6. Zaɓi restore point ɗin da kake so ka koma, musamman wanda aka ƙirƙira kafin matsalar ta fara.
7. Danna “Next” sannan “Finish” don tabbatarwa.
8. Windows zai sake kunnawa, sannan ya mayar da tsarin zuwa restore point ɗin da ka zaɓa.
Bayan an gama, za ka ga sako cewa an kammala System Restore cikin nasara. Idan matsalar ta shafi software ko sabuntawa ne, yawanci za ta kau.
Matakai na Amfani da System Restore a Windows 11
Tsarin yana kusan iri ɗaya da na Windows 10, amma akwai ɗan bambanci a hanyoyin shiga.
1. Danna maɓallin “Start” sannan ka rubuta Recovery.
2. Zaɓi Recovery Options daga cikin sakamakon.
3. A cikin zaɓuɓɓukan, danna “Open System Restore”.
4. Za ka ga taga mai kama da ta Windows 10. Danna “Next”.
5. Zaɓi restore point daga jerin. Za ka iya duba “Scan for affected programs” domin ganin irin canje-canje da za a mayar.
6. Danna “Next” sannan “Finish” domin fara tsarin.
Windows 11 zai sake kunnawa kuma ya dawo da tsarin baya kamar yadda yake a ranar restore point ɗin. Wannan tsari yawanci baya ɗaukar fiye da mintuna 10–20 gwargwadon girman bayanan.
Idan Windows Bai Buɗe Ba (Advanced Recovery)
Wasu lokuta matsalar tana hana Windows buɗewa gaba ɗaya. A irin wannan yanayi, za ka iya amfani da System Restore ta hanyar Advanced Startup Environment.
1. Kunna kwamfuta. Lokacin da tambarin Windows ya bayyana, danna maɓallin wuta (Power) ka riƙe shi har sai PC ya kashe.
2. Maimaita hakan sau biyu ko uku har sai Windows ya shiga “Recovery Mode”.
3. Zaɓi Troubleshoot daga allon.
4. Daga nan, zaɓi Advanced options.
5. Danna System Restore.
6. Zabi account ɗinka, shigar da kalmar sirri idan ana bukata.
7. Zaɓi restore point sannan ka ci gaba da matakai kamar yadda aka bayyana a sama.
Wannan hanya tana aiki ne ko da Windows ɗinka baya buɗewa ta al’ada, matuƙar restore points suna akwai a cikin tsarin.
-
Gargadi da Shawarwari
Kafin yin System Restore, ka tabbata ka ajiye muhimman takardunka a waje, koda yake System Restore baya goge su.
Kada ka katse tsarin restore idan ya fara, domin hakan na iya kawo matsala ga tsarin Windows.
Idan restore ɗin bai magance matsalar ba, za ka iya gwadawa da wani restore point ko yin reset gaba ɗaya.
Ka tabbatar an kunna System Protection domin Windows ya riƙa ƙirƙirar restore points a nan gaba.
System Restore hanya ce mai sauƙi da inganci wajen dawo da tsarin Windows baya idan matsala ta taso. Yana adana lokaci da ƙoƙari idan aka kwatanta da sake shigar da Windows daga farko. Ta hanyar fahimtar yadda ake amfani da shi a Windows 10 da 11, da kuma yadda ake shiga Recovery Mode idan tsarin bai buɗe ba, za ka iya warware matsaloli da kanka ba tare da kiran technician ba.
✍️ Nuhu Saad Kumurya