Ranar da aka wallafa: Agusta 5, 2025
Marubuci: Nuhu Saad Kumurya
Bayan rikicin kwanaki 12 da ya gabata tsakanin Iran da Isra’ila, duniya na ci gaba da sa ido sosai kan ci gaban da kasar Iran ke samu a fannin makaman kare dangi. A cikin wannan makala, za mu duba yadda sabon makamin Khorramshahr-5 ke barazana ga manyan kasashe, musamman Amurka da Isra’ila, da kuma irin matsayin da hakan ke kara wa Iran a fagen fasahar soji.
Khorramshahr-5 wani sabon nau'in Intercontinental Ballistic Missile (ICBM) ne da kasar Iran ta kirkiro. Wannan makami yana da ikon kai hari daga Iran zuwa ko'ina cikin duniya, har da yankin Amurka. Ana hasashen zai iya daukar kunshin nukiliya tare da tafiya nisan kilomita 12,000 (kimanin mil 7,456).
Wannan makami yana cilla gudu har zuwa Mach 16 wato kimanin 20,000km/h. Saboda irin wannan sauri, yana iya kai hari cikin lokaci ƙalilan. Baya ga haka, yana da basirar gujewa makaman kariya na abokan gaba, wanda ke nuna cewa Iran ta kai matakin fasaha da bai kamata a raina ba.
Amurka, Isra’ila, da kasashen Turai sun nuna babbar damuwa kan wannan ci gaba. Kodayake Iran bata fitar da cikakken bayani ba, masana tsaro daga kasashen duniya sun tabbatar da cewa Khorramshahr-5 ya kai matakin makamin ICBM. Wannan yana nufin cewa Iran ta shiga jerin kasashe kalilan a duniya da suka mallaki irin wannan karfin tsaro.
Tsawon lokaci Iran na taka rawa wajen bunkasa fasahar gida ba tare da dogaro da kasashen waje ba. Injiniyoyin Iran mutane ne masu himma, ilimi, da kishin kasa, wadanda ke amfani da duk wata hanya domin kare kasarsu daga barazanar makiya. Wannan sabuwar fasaha ta makami na daga cikin manyan dalilan da ke sa Isra’ila cikin tsoro da fargaba.
Iran ta ƙi bayar da cikakken bayani game da makamin Khorramshahr-5, amma hotunan da aka fitar da kuma bayanan da masana suka iya tattarawa sun tabbatar da cewa wannan makami ne mai girma da ƙarfin gaske. Hakan ya tabbatar da cewa Iran tana da cikakkiyar damar kare kanta da ma kawo hari ga wanda ya kuskura ya tayar da husuma.
Wannan ci gaba na Iran ya nuna muhimmancin samun shugabanni da injiniyoyi masu kishin kasa. A Najeriya, muna da dalilin yin addu’a da kuma neman shugabanni da zasu mayar da hankali wajen inganta tsaron kasa da dogaro da kai a fagen kere-kere. Injiniyoyi ne ginshikan gina kasa mai karfi da kwarjini.
Masu karatu zasu iya amfani da Artificial Intelligence kamar ChatGPT, Perplexity, ko Claude don bincike. Haka kuma, shafukan yanar gizo kamar Google News na dauke da cikakken bayani kan makamin Khorramshahr-5 da irin matsayinsa a duniya.
Iran ta kai wani sabon matsayi a fagen tsaro da makaman zamani. Samun makamin ICBM irin Khorramshahr-5 ba karamin ci gaba bane. Wannan yana kara tabbatar da cewa kasashe masu dogaro da fasaha da ilimi na iya tsayawa kai da fata wajen kare kasarsu. Allah ya azurta Najeriya da shugabanni da injiniyoyin da za su karbi darasi daga irin wannan ci gaba.
Idan ka ji dadin wannan bayani, raba shi a WhatsApp, Facebook, da Twitter. Zai iya zama darasi ga matasa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da fasaha.
© Nuhu Saad Kumurya - Kumurya Media Inc.