![]() |
BBC Hausa |
Ta fito ƙarara cewa Isra'ila za ta amsa manyan tambayoyi waɗanda ba za su tafi haka kawai ba.
Tana kuma fuskantar shari'a kan zargin kisan kare dangi a gaban Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta ICC, kuma an taƙaita wa Firaministan ƙasar tafiye-tafiye saboda an bayar da sammacin kama shi kan zargin aikata laifukan yaƙi.
Ƴan siyasar ɓangaren adawa a cikin Isra'ila sun zargi Netanyahu kan jagorantar batutuwa da suka shafi yaƙi da kuma sanya a mayar da Isra'ila saniyar ware.
Hujjoji kan alkaluman waɗanda aka kashe a Gaza
Hujjoji kan abubuwan da ke faruwa a Gaza ya fara ne da alkaluman waɗanda abin ya shafa. A ranar 7 ga Oktoban 2023 Hamas ta kutsa cikin Isra'ila, inda ta kashe mutum 1,200. Sama da 800 daga cikinsu sun kasance farar hula.
Sauran sun haɗa da mambobin jami'an tsaron Isra'ila, masu ba da taimakon gaggawa da ma'aikatan ƙasashen waje. Kusan mutum 250, ciki har da waɗanda ba Isra'ilawa ba - aka yi garkuwa da su zuwa Gaza.
Sai dai alkaluman sun ɗan bambanta kaɗan, amma an yi imanin cewa har yanzu akwai mutum 54 da suka rage a Gaza, inda aka ce 31 sun mutu.
Bayyana aininin alkaluman Falasɗinawa da aka kashe a cikin Gaza yana da matukar wahala.
Isra'ila ta taƙaita zirga-zirga a cikin Gaza, kuma ba a iya kai wa wasu sassa na arewacin zirin.
Sabbin alkaluman da ma'aikatar lafiya a Gaza ta fitar, sun nuna cewa Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 54,607 tare da jikkata 125, 341 daga harin 7 ga Oktoban 2023 zuwa 4 ga Yunin wannan shekara.
Alkaluman ba su bambanta fararen hula daga mambobin Hamas ba da sauran ƙungiyoyin mayaƙa.
A cewar Unicef, zuwa watan Janairun wannan shekara, ISsra'ila ta kashe yara Falasɗinawa 14,500 a Gaza; an raba 17,000 da iyayensu ko kuma mayar da su marayu; kuma Gaza ce ke mai yawan yaran da aka yanke wa kafa ko hannu a duniya.
Isra'ila da Amurka sun yi ƙoƙarin nuna shakku kan rahotannin waɗanda yaƙin Gaza ya shafa daga ma'aikatar, saboda cewa Hamas ce ke iko da ita.
Sai dai Majalisar Ɗinkin Duniya, jami;an diflomasiyya na amfani da alkaluman da ma'aikatar ke fitar wa, kai har ma da jami'an leƙen asirin ƙasar, kamar yadda Isra'ila ta bayyana.
Lokacin da aka duba alkaluman ma'aikatar a yaƙin baya, an ga ya yi daidai da na wasu.
Fararen hula a Gaza sun samu sararawa na ƙankanin lokaci a farkon shekarar nan bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta. Sai dai bayan ƙasa cimma yarjejeniyar kan tsagaita wuta ta tsawon lokaci, Isra'ila ta koma kai hare-hare ranar 18 ga watan Maris tare da kaddamar da sabon farmakin soji wanda ta ce shi zai samar da nasarar da take nema.
Isra'ila ta saka tsauraran takunkumai kan shigar da abinci da kuma agaji Gaza tun soma yaƙin, kuma ta toshe hanyar kai su baki-ɗaya daga watan Maris ɗin wannan shekara.
Ganin cewa Gaza na daf da faɗa wa cikin matsalar yunwa, ta fito ƙarara cewa Isra'ila ta saɓa wa dokokin da suka buƙaci a kare fararen hula, ba saka su cikin yunwa ba.
Wani jami'in gwamnatin Birtaniya ya faɗa wa BBC cewa Isra'ila na amfani da yunwa "a matsayin makamin yaƙi".
Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz, ya fito fili ya bayyana cewa sun toshe hanyar kai abinci ne domin "matsa lamba" kan Hamas ta saki waɗanda take garkuwa da su - ta kuma amsa shan kaye.
Amfani da abinci a matsayin makami, lafin yaƙi ne.
Gazawar jin-kai
Yaƙi ba abu bane mai kyau. Na kasance a Geneva domin haɗuwa da jami'ar diflomasiyyar Switzerland, Mirjana Spoljaric, wadda ita ce shugabar ƙungiyar agaji ta Red Cross ICRC.
Ta yi imanin cewa lamarin zai iya ƙara muni; kuma akwai alamun cewa dukkan ɓangarori na take yarjejeniyar Geneva, kuma wannan ya aika sakon cewa za a iya watsi da dokokin yaƙi a rikice-rikice a faɗin duniya.
Ta kuma yi gargaɗin cewa "muna take dokokin da suka kare kowane irin ƴancin ɗan'adam".
Mun zauna da ita domin tattaunawa a wani ɗaki, ida ta ce lamarin da ke faruwa a Gaza ya fi na jahannama.
"Ana ci gaba da samun gazawar jin-kai a Gaza," in ji Ms Spoljaric. "Abubuwa na durkushewa. Ba za mu ci gaba da zuba ido muna ganin abin da ke faruwa ba. Abin ya saɓa wa tunani, mutunta ɗan'adam da ma doka. Irin taɓargazar da ake yi da matsananciyar wahala da mutane ke ciki ba za ta misaltu ba."
Ta ƙara da cewa, duniya ta zuba ido tana kallo an mayar da al'ummar Falasɗinawa kamar dabbobi.
"Abun kaɗuwa ne matuka... Abin zai dawo ya dame mu. Muna ganin abubuwan da ke faruwa da za su saka duniya ta zama cikin masifa fiye da yankin da abin ke faruwa."
Na tambaye ta kan hujjar da Isra'ila ta bayar cewa tana yaƙi don kare kanta da kuma wargaza ƙungiyar ƴan ta'adda da ta kai mata hari tare da kashe mutane ranar 7 ga Oktoba.
"Wannan ba hujja ba ce ra rashin mutuntaka da kuma take yarjejeniyar Geneca," in ji ta. "Babu ɓangaren da ke da hurumin karya dokoki, ko wane yanayi aka shiga, kuma hakan yana da muhimmanci saboda dokoki ne na kare ƴancin ɗan'adam karkashin yarjejeniyar Geneva.
"Yaron da ke Gaza yana da damar kariya irin wanda yaron da ke Isra'ila ke da shi a karkashin arjejeniyar Geneva."
Mirjana Spoljaric, ta yi magana cikin nutsuwa. Red Cross na ɗaukar kanta a matsayin ƙungiyar ba-ruwana; tana ƙoƙarin aiki da duka ɓangarori a yaƙe-yaƙe.
Sai dai ba ta nuna matsayin ba-ruwana ba a ɓangaren irin hakkokin da ya kamata ɗan'adam ya samu, kuma ta damu matuka cewa an lalata waɗannan hakkoki ta hanyar take dokokin yaƙi a Gaza.
'Za mu mayar da su tamkar ɓaraguzai'
A yammacin ranar 7 ga Oktoban 2023, yayin da sojojin Isra'ila ke ƙoƙarin fatattakar mayaƙan Hamas da suka kutsa ƙasar, Benjamin Netanyahu ya yi wani jawabi ga al'ummar Isra'ila da kuma duniya.
Da yake jawabi daga tsakiyar Tel Aviv, ya zaɓi amfani da kalamai da za su kwantar wa ƴan Isra'ila rai da kuma razana abokan gaba. Da kuma yadda Isra'ila za ta fuskanci yaƙin da kuma kare ƙasarta.
Ya ce karshen Hamas ya zo. "Za mu wargaza su kuma za mu rama abin da suka yi mana musamman wannan bakin rana a tarihinmu na far wa Isra'ila da al'ummarta.
"Za mu mayar da dukkan wuraren da Hamas ke amfani da su wurin ɓoyewa da kuma birnin zuwa ɓaraguzai.
Netanyahu ya yaba wa ƙawayen Isra'ila da suke mara mata baya, inda ya ambaci Amurka da Faransa da kuma Birtaniya. Ya yi magana da su, in ji shi, "domin tabbatar da cewa an ɗauki mataki".
Sai dai a yanzu, Birtaniya da Faransa da Canada na son Isra'ila ta kawo karshen farmakin da take yi a Gaza nan take.
Ranar 19 ga watan Mayu, Firaminista Sir Keir Starmer da Mark Carney, da kuma shugaba Emmanuel Macron suka bayyana cewa, "Mun kasance muna goyon bayan Isra'ila don ta kare kanta kan ta'ddanci. Sai dai wannan farmaki ya wuce tunani... Ba za mu zuba ido muna ganin gwamnatin Netanyahu na ɗaukar matakai da suka wuce tunani ba."
Takunkumai na iya bin baya. Birtaniya da Faransa na duba yiwuwar ganin sun amince ƙasar Falasɗinu.
Yaƙi da ɗaukar fansa
Netanyahu ya yi amfani da kalmar ɗaukar fansa a jawabinsa bayan harin 7 ga Oktoba da Hamas ta kai.
Falasɗinawa na ganin batun yaƙi da kuma wargaza al'ummarsu tun 1948 lokacin da Isra'ila ta samu ƴancin kai, abin da suka kira da bala'i.
Sai dai Netanyahu da sauran ƴan Isra'ila da magoya bayansu sun danganta harin da Hamas ta kai da irin cin zarafi da Yahudawa suka fuskanta a Turai, wanda ya janyo ƴan Nazi suka kashe Yahudawa miliyan shida a Holocaust.
Netanyahu ya yi amfani da irin waɗannan misalai wajen mayar da martani ga Macron lokacin da ya faɗa a watan Mayu cewa "abin kunya ne" toshe hanyar kai agaji Gaza da Isra'ila ta yi wanda "ba za a lamunta ba".
Firaministan na Isra'ila ya ce Macron "ya sake nuna goyon baya ga ɓangaren ƙungiyar ta'addanci, inda kuma yake son ya nuna mashaya jini.
Kalmar mashaya jini abu ne da aka daɗe ana amfani da a Turai, ida ake zargin Yahudawa da kashe Kiristoci, musamman yara domin amfani da jininsu wajen yin tsafe-tsafe.
Bayan kashe wasu ma'aurata waɗanda ke aiki da ofishin jakadancin Isra'ila a Washington, ɗan bindigar da ya harbe su ya ce, "Na yi haka ne don Falasɗinawa, Na aikata haka don Gaza."
A wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafin X, Netanyahu ya ce: "Na faɗa wa shugaba Macron, Firaminista Carney da Firaminista Starmer cewa: Idan makisa, masu fyaɗe, masu kashe jarirai da masu garkuwa suka gode muku, to kuna ɓangaren rashin adalci. Kuna ɓangaren rashin mutunta ɗan'adam da kuma tarihi.
"Tsawon shekara 18, mun fuskanci Falasɗinawa. Ana kiran wurin Gaza. Kuma me muka samu? Babu. Mun samu yanayin kisan Yahudawa da yawa tun lokacin Holocaust.
Amurka: Ƙawar Isra'ila mai muhimmanci
Isra'ila ba za ta iya yin faɗa a Gaza ta hamyar amfani da dabarunta kaɗai ba, har sai ta samu taimakon soji, kudaɗe da kuma diflomasiyyar Amurka. Shugaba Donald Trump ya nuna alamun rashin hakuri, abin da ya tilastawa Netanyahu barin Gaza ta kusa faɗawa cikin yunwa.
Shi kansa Netanyahu ya ci gaba da goyon bayan shirin Trump na mayar da Gaza zuwa "wani yanki batu da aka yi Alla-wadai kansa. Hakan ya sa Netanyahu ya tilastawa Falasɗinawa da dama barin Gaza, wanda zai iya zama laifin yaƙi.
Ƙawayen Isra'ila na son maye gurbinsu da Yahudawa ƴan kama wuri zauna.
Shi kansa Trump ya yi shiru kan batun. Sai dai goyon bayan da gwamnatin Trump ke bai wa Isra'ila a Gaza, bai ragu ba.
A ranar 4 ga watan Yuni, Amurka ta ki amincewa da buƙatar kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya cewa "a cimma yarjejeyar tsagaita wuta ta dindindin", sake waɗanda ake garkuwa da su da kuma ɗage takunkumai kan ayyukan jin-kai.
Sauran mambobi 14 sun amince da buƙatar.
Washegari Amurka ta saka wa alkalan kotun ICC huɗu takunkumai don mayar da martani kan sammacin kame.
Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya ce yana kare ƴancin Amurka da Isra'ila kan "matakai ba bisa ka'ida ba".
Isra'ila da gwamnatin Trump sun yi watsi da batun cewa dokokin yaƙi daiɗai sukje ga dukkan ɓangarori, saboda sun yi iƙirarin cewa ba daidai bane kwatanta Hamas da Isra'ila.
Batun tambayar kisan kare dangi
Tambayar cewa ko Isra'ila na aikata kisan kare dangi a Gaza ya janyo kaɗuwa da fushi daga Isra'ila da magoya bayanta, karkashin jagorancin Amurka. Lauyoyin da suka yi imanin cewa hujjojin ba su yi goyon bayan zargin ba, sun kalubalanci batun da Afirka ta Kudu ta gabatar a kotun ICC, kan zargin aikata kisan kare dangi kan Falasɗinawa.
Sai dai tambayar ba za ta tafi haka nan ba.
Wani mai goyon bayan Netanyahu Boaz Bismuth ya amsa tambayar kan kisan kare dangi kamar haka.
"Ta yaya za ka zarge mu da kisan kare dangi lokacin da al'ummar Falasɗinawa ke girma, ban san adadin lokaci ba? Ta yaya za ka zarge mu da shafe wata kabila lokacin da muke kare al'ummar da ke cikin Gaza? Ta yaya za ka zarge ni bayan rasa sojoji a ƙoƙarin kare abokan gabana?"
Yana da matukar wahala a iya tabbatar da ko cewa an aikata kisan kare dangi; ya kamata lauyoyi masu shigar da ƙara su fayyace abubuwa ƙarara. Sai dai lauyoyi da ke kan gaba waɗanda suka shafe gomman shekaru suna duba batutuwan shari'a domin ganin ko akwai kamshin gaskiya a lamarin, sun yi imanin cewa ba lallai a jira batun da ya fara tun Janairun bara ba da Afrika ta Kudu ta gabatar a kotun ICC.
Wani yaro zaune cikin ɓaraguzai a Gaza bayan harin Isra'ila a watan Yuni
Da alamu, za a iya samun tsagaita wuta. Ba zai kawo karshen rikicin ba. Batun kisan kare dangi a ICJ zai tabbatar da hakan. Shin za kotun ICC za ta iya kama Netanyahu da Yoav Gallanta.
Muddin ƴan jarida da masu binciken lafiukan yaƙi suka samu damar shiga Gaza, za su binciko hujjoji da dama da za su nuna abin da ya faru.
Waɗanda suka je Gaza tare da MDD ko kuma tawagogin likitoci sun ce ko da mutanen da suka ga yaƙe-yaƙe zai yi wuya su iya bayyana ɓarnar Gaza; an jefa mutane da dama cikin ƙunci da wahala.