Notification texts go here Contact Us Buy Now!

Hanyoyin kare kai daga masu ƙwacen waya

 

Hanyoyin kare kai daga masu ƙwacen waya
BBC Hausa



Hanyoyin kare kai daga masu ƙwacen waya

Yanzu haka ƙwacen waya na daga cikin dalilan da ke janyo rasa rayuka a arewacin Najeriya inda da wuya gari ya waye ba tare da samun labarin rasuwar wani ko jikkata ba sakamakon ayyukan masu ƙwacen waya.


Labarin da ya ɗaga hankalin jami'an tsaro da na ƴan Najeriya shi ne na kisan wani babban sojan ruwa a gadar Kawo da ke Kaduna sakamakon caka masa wuka da wani ɓarawon waya ya yi a ƙirjinsa.


A jihar Gombe ma masu satar wayar sun caka wa wani bawan Allah mai suna Alhaji Ahmadi Aliyu Umar wuƙa al'amarin da ya yi sanadiyyar rasa ransa, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.


Ko a shekarar 2024 sai da masu ƙwacen wayar suka yankewa wani ɗan yatsa a ƙokarinsu na ƙwace wayar daga hannunsa lokacin da yake cikin Adaidaita Sahu a birnin Kano.


Waɗannan dai kaɗan ne daga cikin irin kisa masu yawa da ake yi sakamakon ƙwacen waya

Hanyoyi uku na kariya daga masu ƙwacen waya

Auwal Bala Durumin Iya, wani masanin tsaro a birnin Kano ya bayyana hanyoyi guda uku na kariya daga ƙwacen waya musamman idan ƙaddara ta saka sun ritsa da kai to akwai abubuwa guda uku da ya kamata mutum ya yi bisa la'akari da tazarar da ke tsakaninku da ɓata-garin.


Tazarar mita biyu: Idan tazarar da ke tsakaninka da masu ƙwacen wayar to kawai ka miƙa musu wayar don ka tsira da rayuwarka alabashi daga baya mutum sai ya ɗauki hukuncin da zai ɗauka na gudu ko kuma na neman haƙƙi ya danganta da yadda dama ta ba ka.

Tazarar mita huɗu: Idan ya zamana ba za su iya miƙa hannunsu ya taɓa ka ba a lokaci guda ba saboda haka ba za su iya afka maka ba to kana da zaɓi. Na gudu ko kuma yin ihu domin jan hankalin jama'a.

Tazarar mita shida: Duk inda ka ga mita shida tsakaninka da masu ƙwacen waya to ka yi ihun da zai janyo hankalin jama'a ko kuma samun wani abun da za ka kare kanka sannan kuma kana da zaɓin guduwa.

Masanin tsaron ya kuma ƙara da bayar da wasu shawarwari da ya ce idan mutum ya riƙe su to Allah zai kare shi daga shiga tarkon masu ƙwacen wayar.


Gujewa wurin da babu jama'a: Ya kamata mutane su guji shiga wuraren da babu jama'a sosai kasancewar mafiya lokuta su kan kasance maɓoyar ɓata-gari. Idan kuma mutum tsautsayi ya sa ya samu kansa a wurin to akwai dabarun da ya kamata ya bi. Ka da mutum ya tsaya a wurin kuma ka da ka yi gudu ko ka tafi a hankali. Abin da ake so ka yi sauri inda hakan zai nuna wa ɓata-garin cewa ka san wurin ba shi da kyau kuma a shirye kake ka ɗauki matakin kare kai.

Gujewa bayyana waya: Idan mutum ya shiga cikin jama'a musamman taro to ka da ya bayyana wayarsa ta hanyar fito da ita da kiraye-kiraye a bainar jama'a ko kuma yin amfani da tufafi shara-shara da ke nuna yanayin wayar. Nuna wayar a fili na jan hankalin masu ƙwacen wayar.

Kula da lokaci: Ya kamata mutane su lura da lokacin da za su rinƙa mu'amila a waje. Misali fita da duku-duku na taimaka wa masu ƙwacen waya. Haka ma idan mutum ya yi dare ya wuce ƙarfe 10 to akwai yiwuwar haɗuwa da masu ƙwacen waya. Sannan a guji hawa abin hawan da zai bi da mutum ta titunan ƙetare (by-pass) ko kuma gadoji da wurare masu duhu da daddare.

Dalilai huɗu da suka sa ƙwacen waya yake da sauƙi

Auwal Bala Durumin Iya masanin harkar tsaron ya lissafa dalilai guda uku da ya ce su ne ke janyo yawan ƙwace waya.


Yawaitar waya: Aƙalla kaso 70 cikin 100 na al'ummar Najeriya yanzu haka suna da waya. Wasu ma ba guda ɗaya ba. Saboda haka yawaitarta ya sa kowa ya san muhimmancinta musamman idan aka sayar da ita.


Sauƙin saye: Kasancewar waya ta yi yawa a tsakaninin al'umma abin da ya sa a duk wurin da aka ɗaga waya to za a samu mai saye. "Idan har ka ɗaga waya kuma cikin farashi mai sauƙi to lallai za a samu mai saye."


Ɗaukar ido: Yawancin dalilin da ya sa ake ƙwacen waya shi ne tana da ɗaukar hankali kuma da zarar mutum ya fito da ita a inda babu jama'a kuma a idanun masu ƙaunar wayar to da wuya ya mayar da ita aljihunsa.


Sauƙin kwace: Waya kasancewarta ba ta da girma tana da sauƙin ƙwacewa ko dai a warce ta ko kuma a tsorata mutum a ƙwace cikin lokaci ƙanƙane.


Mafita

Masanin harkar tsaron ya ce hanyoyi biyu a ganinsa da suka kamata a bi domin warware matsalar.


Dokar ta ɓaci: Ayyana dokar ta ɓaci kan ƙwacen waya tare da fito da zartar da hukunci mai tsanani ga duk wanda aka samu da laifin aikata ƙwacen wayar.

Wayar da kai kan illar ƙwacen waya: Dole ne a ɗauki matakai daban-daban na al'umma a rinƙa wayar da kai musamman yara da ke tasowa kasancewar a yanzu haka masu sata da ƙwacen wayar yara ne ƙanana. Iyaye da sarakunan gargajiya da malamai da ƙungiyoyi su rinka faɗakar dangane da illar ƙwace wayar.

About the Author

Webmaster | Youtuber | Freelancer | Programmer | Sm Engineer | Blogger | Muslim | Sunni

Post a Comment

Cookie Consent
We serve cookies on this site to analyze traffic, remember your preferences, and optimize your experience.
Oops!
It seems there is something wrong with your internet connection. Please connect to the internet and start browsing again.
AdBlock Detected!
We have detected that you are using adblocking plugin in your browser.
The revenue we earn by the advertisements is used to manage this website, we request you to whitelist our website in your adblocking plugin.
Site is Blocked
Sorry! This site is not available in your country.