Yau muka samu wata babbar nasara da muka dade muna fatan samu a aikin Da’awah. Wani babban jigo, shugaba mai arziki, kuma mutum mai farin jini a cikin al’umma ya karɓi Musulunci tare da daruruwan mabiyansa.
A cikin kalamansa mai cike da tausayin zuciya, ya ce:
"A shekarun baya mun toshe kofa wa Musulunci. Amma yau sai gamu a cikinsa. Wallahi na shigo Musulunci domin in yi wa Musulunci!"
Wannan kalma ta nuna yadda Allah ke shiryar da zukata a lokacin da ya dace.
Shigowarsa Musulunci wata gagarumar nasara ce ga aikin Da’awah kuma farka ne ga lagon kafirci da aka shafe shekaru ana yinta. Allah kadai yasan irin yawan mutanen da za su shigo Musulunci ta sanadin sa daga yau har zuwa gobe.
Kofa a bude take!
Ga duk wanda ke da hali, ana kira da taimakawa wannan Da’awah da duk abin da Allah ya hore masa – da dukiyarsa, lokaci ko addu’a. Wannan tafiya ce mai albarka, kuma Allah yana saka lada mai girma ga masu taimakawa aikinSa.
Tura Sadaqa:
Sterling Bank
Al-Imaan Islamic Foundation