![]() |
Image credit:Facebook |
🚨 | Kana kan LinkedIn?
Wato LinkedIn can do wonders.
LinkedIn wani social media community da gaskiya bayyi tasiri a wajen mu ba mu yan arewa. Kuma mutane suna amfani da shi daga kusan ko ina a duniya. Waje ne da kai tsaye zan iya cewa is a professional platform wato ma'ana gurine na yan boko, ma'aikata, yan kasuwa, CEOs da sauransu. Ba kamar Facebook bane ballantana kaje kayi ta yin molanta. Wajene da ake sharing job opportunities, online research, courses, trainings, recruitment da sauransu. Idan kana son aiki a cooperate organisation, NGOs, Universities, firms, nan ne zaka je kayi Register don samun updates akai.
That's not all, LinkedIn yana baiwa users dama su sanya bayanai akan educational background nasu, working experiences, achievements, publications, skills da sauransu, don idan mutum ya shiga yaga tarihinka da kuma waye kai a dan kankanin lokacin kuma a wadace. Sannan kai ma idan kana neman karin bayani a wadace akan wani expert ko professional, zaka iya shiga ka duba har ma kayi magana da shi professional ko Academically.
Nace a sama LinkedIn can do wonders. Abinda yasa na fadi shine, ban taba sanin tasirinsa ba, ko mahimmancisa, ko na dauke shi more serious sai da abu biyu suka faru. Na daya ana considering dina for wani position, although Maganar is premature. So sai suka shiga LinkedIn suga duba bayanaina. Bayan sun duba sai suka kira ni. Suna kira sai suka ce mun ga bayananka a LinkedIn, very fascinating. Sai nace aw dama mutane suna duba LinkedIn dina? Na biyu last Saturday nayi program a Freedom Radio. Presenter na shirin, video na ya gani a Facebook, kuma kawai sai ya shiga LinkedIn sanin cewa ni professional ne. Sai ya duba ni a can. Acan ne ya gano cewa a cikin LinkedIn followers dina akwai abokinsa, sai ya masa magana daga nan aka samo masa Number ta.
So ashe kenan mutane da yawa sune duba mu a LinkedIn din da ma wasu guraren. Kuka yana da kyau a duk sanda zaka saka bayanan ka kar kasa bayanan karya ko bayanai marasa amfani. Domin baka san wa zai shiga ya duba ka ba. A karshe bayan LinkedIn akwia wani research platform da ya kamata ace duk wani mai yin Research yana kai, domin yana sa mutane su gane ka akan field dinka kuma su sanka akan aikinka. Sunansa ResearchGate. Shima yana da kyau a shiga, kuma a zuba bayanai na Research don samun haskawa a research arewa.
Allah ya bamu sa'a.
----
Muhammad Ubale Kiru
#MuhdKiru