Illolin Amfani da Mosquito Coil da Yadda Ake Amfani da Shi Lafiya
A gidajenmu na karkara da birane, “Mosquito Coil” ya shahara sosai a matsayin hanya ta yaki da sauro. Amma shin mun san yadda yake aiki da kuma yadda ake amfani da shi lafiya? Wannan rubutu zai bayyana muku gaskiya game da Mosquito Coil, illolinsa, da hanyoyin kariya ga lafiyar jiki.
Menene Mosquito Coil?
Mosquito Coil wani kalar kayan konewa ne da ake kunna shi domin fitar da hayaƙi da ake tsammani zai hana sauro shigowa ko cizon mutum. Yana fitowa da siffar zobe mai lankwasa kamar leda, kuma yakan kone a hankali na tsawon sa’o’i.
Shin Mosquito Coil Na Kashe Sauro?
Akasin yadda ake tunani, Mosquito Coil baya kashe sauro kai tsaye. Abin da yake yi shi ne rage wa sauro ƙarfi da kuma hana su kusantar jiki na ɗan lokaci. Wannan yana nufin cewa idan kana bukatar maganin da zai kashe su gaba ɗaya, sai ka nemi wani magani na musamman kamar feshi ko na lantarki.
Illolin Hayaƙin Mosquito Coil ga Lafiyar Jiki
Hayaƙin Mosquito Coil yana ɗauke da sinadarai masu sa hayaƙi ya yadu cikin ɗaki. Wasu daga cikin wadannan sinadarai na iya haifar da matsaloli masu tsanani, musamman ga waɗanda ke da raunin numfashi.
Ga wasu daga cikin illolinsa:
- Shaƙewar hanci da cushewa
- Tari da ciwon kirji
- Ciwo a makogwaro
- Ciwon ciki, musamman ga yara
- Ƙara tsananta cututtuka kamar asthma
- Yana iya haddasa cutar kansa idan ana amfani da shi akai-akai
- Yana iya haifar da gobara idan aka bar shi ba tare da kula ba
Yadda Ake Amfani da Mosquito Coil Lafiya
Idan har zaka yi amfani da Mosquito Coil, to dole ka kula da waɗannan abubuwa domin kare kanka da iyalanka:
- Ka kunna Mosquito Coil sannan ka buɗe ƙofofi da tagogi domin iska ta shiga da fita.
- Kada ka sa shi kusa da inda yara ke kwana ko masu fama da cututtukan numfashi.
- Ka tabbatar kana da kayan kashe gobara idan ya faru da bazata.
- Kada ka kunna shi a ƙarƙashin labule ko kusa da kayan da zasu iya kama da wuta da sauri.
Madadin Amfani da Mosquito Coil
Idan kana son kare kanka daga sauro ba tare da illolin hayaƙi ba, zaka iya amfani da waɗannan:
- Ragar sauro (Mosquito Net): Wannan hanya ce mafi lafiya, musamman ga yara da tsofaffi.
- Electric mosquito repellent: Na’urar lantarki da ke fitar da ƙamshi ko sauti da ke korar sauro.
- Maganin feshi: Akwai magungunan feshi da ke kashe sauro da tsawon lokaci.
- Tsaftace muhalli: Sare ciyawa, zubar da ruwa a cikin kwantena ko tukwane, da rufe kwantena masu ruwa na hana sauro haihuwa.
Kammalawa
Mosquito Coil na iya zama taimako a wasu lokuta, amma yana tattare da haɗari ga lafiya idan ba a kula ba. Kafin ka yanke shawarar amfani da shi, ka tabbata cewa kai da iyalinka ba ku cikin haɗarin da ya ke janyo wa. Kula da tsafta da amfani da hanyoyi masu lafiya ya fi amfani da abin da zai iya cutar da kai.
⚠️ Ka tuna: Facebook ba asibiti ba ne. Idan kana fama da matsalar shaƙewar numfashi ko wani ciwo da ya shafi numfashi, ka nemi gaggawar kulawa a asibiti mafi kusa da kai.
Rubutawa: Alhassan Mai Lafiya