Shugaban Najeriya Ya Bada Umarnin Daukar Ma'aikata 30,150 a Hukumi Biyar – Ga Yadda Zaka Nemi Aikin
🟣 Shugaban Najeriya Ya Amince da Daukar Ma’aikata Mutum 30,150 a Cikin 2025
A wani mataki na rage rashin aikin yi a Najeriya, gwamnatin tarayya ta amince da daukar sabbin ma’aikata har mutum 30,150 a wasu muhimman hukumomin gwamnati guda biyar. Wannan mataki zai kara damar samun aiki ga matasa da dama a fadin kasar.
🔰 Jerin Hukumomin da Za Su Dauki Ma'aikata
✅ 1. Nigerian Correctional Service (NCoS)
Hukumar gyaran hali ta Najeriya za ta dauki mutum 5,150. Wannan hukumar na da alhakin kula da gidan yari da gyaran halin fursunoni.
✅ 2. Nigerian Immigration Service (NIS)
Hukumar shige da fice za ta dauki mutum 10,000. Wannan dama ce ta musamman ga masu sha’awar aikin iyaka da kula da shige da fice.
✅ 3. Nigerian Security and Civil Defence Corps (NSCDC)
Hukumar tsaro ta farin kaya zata dauki mutum 10,000. NSCDC na taka rawar gani wajen samar da tsaro a cikin gida da kiyaye kadarorin gwamnati.
✅ 4. Federal Fire Service (FFS)
Hukumar kashe gobara ta Najeriya zata dauki mutum 5,000. Wannan dama ce ga masu sha’awar aikin ceto da taimakon gaggawa.
✅ 5. Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB)
Ita kanta hukumar da ke kula da wadannan hukumomin za ta dauki mutum 209 domin cike guraben aiki a ofishinta.
🕐 Yaushe Za a Fara Daukar Ma’aikatan?
Kamar yadda Nasiru Auwalu Eliyasu P’a ya tabbatar, nan da makonni uku (3), za a bude shafin (portal) na neman wadannan ayyukan. Ana shawartar matasa da su fara shiryawa tun yanzu – da takardu, CV da sauran sharuɗɗan da ake bukata.
🔎 Yadda Zaka Taka Mataki:
1. Tsaftace takardunka – kamar Certificate, LGA Certificate, Passport, da sauransu.
2. Koyi yadda ake cike online form (za mu zo da cikakken shafi da zarar an bude).
3. Rijista da farko da zarar an bude portal.
4. Bibiya da bin umarnin hukumar da kake so ka shiga.
💬 Ka Shirya Tsaf? Sai Ka Fara!
Wannan dama ce ta shekara! Idan kana neman aikin gwamnati a Najeriya, wannan shi ne lokacin da ya dace. Kada ka bari a bar ka a baya!
🟠 Kar Ka Manta!
Za mu sanar da link ɗin portal da cikakkun sharuɗɗa da zarar an bude. Ka tabbata ka bi mu ta hanyar:
✅ Shiga WhatsApp Group ɗinmu
✅ Bibiya a shafinmu na Facebook
✅ Karanta updates daga nan kullum
📢 Rarraba Wannan Labari Ga Daukacin Jama’a!
Ka taimaka wa wani ta hanyar tura wannan post ɗin zuwa Facebook, WhatsApp, da Telegram. Zai iya zama hanyar samun aikin rayuwarsa!
✍️ Marubuci:
Nasiru Auwalu Eliyasu P’a
Edita: Nuhu Saad Kumurya – Kumurya Media Inc.
إرسال تعليق