Sharuddan Da Dole YouTube Channel Ta Cika Domin Samun YouTube Play Button Awards (Sabbin Ka’idojin 2025)

  Sharuddan Da Dole YouTube Channel Ta Cika Domin Samun YouTube Play Button Awards (Sabbin Ka’idojin 2025)


Kalli cikakken jerin sharuddan da dole ka cika kafin YouTube ta baka Creator Award (Play Button). Sabbin ka’idoji sun hada da subscriber, originality, da bin dokokin Community Guidelines.


Assalamu Alaikum Warahmatullah,

Yaya kuke, yan uwa?

Muna fatan kowa yana cikin koshin lafiya. Ni ma, da taimakon Allah, ina cikin koshin lafiya. Ga masu bin shafinmu na Naijatech  kullum, tabbas kuna samun sabbin abubuwa da dama da ke inganta rayuwar ku a fannin fasaha.


A yau, zamu tattauna muhimmin batu: Menene YouTube ke bukata kafin ta baka Creator Award ko Play Button?


Akwai sabbin dokoki da dole kowane channel ya cika kafin samun wannan lambar yabo. Ba wai kawai samun subscribers bane zai sa a baka Play Button, akwai wasu muhimmam sharudda da dole a bi.

Kalli cikakken jerin sharuddan da dole ka cika kafin YouTube ta baka Creator Award (Play Button). Sabbin ka’idoji sun hada da subscriber, originality, da bin dokokin Community Guidelines.



Matakan Subscriber Da Ke Samar Da Play Button:


🔘 Silver Play Button – Idan ka kai 100,000 subscribers


🟡 Gold Play Button – Idan ka kai 1,000,000 subscribers


💎 Diamond Play Button – Idan ka kai 10,000,000 subscribers


🔴 Red Diamond Play Button – Idan ka kai 100,000,000 subscribers




---


Sharuddan Da Dole Channel Dinka Ya Cika:


✅ Channel dinka ya kasance mai aiki – dole a sami upload cikin watanni 6 da suka gabata.

✅ Babu wata Community Guideline strike cikin kwanaki 365 da suka wuce.

✅ Ka na bin ka’idojin YouTube Terms of Service.

✅ Channel dinka bai taba samun dakatarwa daga YouTube Partner Program ba.

✅ Ba a taɓa dakatar da channel ɗinka ko haɗa shi da wani account da aka dakatar ba.

✅ Content ɗinka ba ya cike da karya, spam, ko zamba.

✅ Abubuwan da kake sawa dole su kasance na asali (original).

➡️ Channels da ke amfani da compilation, mixing, ko amfani da copyright content na wasu za a iya hana su lambar yabo.



---


Muhimman Bayani:


🔹 Ba lallai bane ka zama cikin YouTube Partner Program (YPP) kafin samun award.

🔹 YouTube na duba kowane channel da hannu kafin bayar da award.

🔹 Creator Awards na sirri ne – ba za a sayar ko raba su ba. Idan aka karya wannan doka, za a iya ladabtar da kai.


Hukuncin Ladabtarwa:


❌ Za a kwace kyautar


🚫 Za a haramta maka samun kyautar nan gaba


❗ Ana iya rufe YouTube ko Google account ɗinka gaba ɗaya

Sharuddan Da Dole YouTube Channel Ta Cika Domin Samun YouTube Play Button Awards (Sabbin Ka’idojin 2025)



Kasashen Da Ba Sa Samun Creator Award:


Wadannan kasashe ba su da damar samun Creator Award daga YouTube:

🇧🇾 Belarus | 🇰🇵 North Korea | 🇸🇾 Syria | 🇨🇺 Cuba | 🇮🇷 Iran | 🇷🇺 Russia | 🇹🇯 Tajikistan | 🇲🇲 Myanmar | 🇻🇺 Vanuatu | 🇸🇴 Somalia | 🇾🇪 Yemen | 🇸🇩 Sudan






Kammalawa:


Idan har kana son samun Play Button daga YouTube, to ka tabbatar kana bin duka wadannan sharudda da dokoki. Idan ba ka bi su ba, to ba za a baka ba.


Muna fatan wannan bayani ya amfanar da kai.


Nuhu Saad Kumurya

Post a Comment

Previous Post Next Post