Karanta: Yadda Zaka Kare Kanka Daga Fake Airdrops

 

Karanta: Yadda Zaka Kare Kanka Daga Fake Airdrops
⚠️ Kar Ka Faɗa Tarkon Fake Airdrop!


Ga Misali da Shaida Cikin Idon Gaskiya 👇🏽


A kwanakin nan, wasu influencers a Facebook sun fara yaɗa wani airdrop mai suna Efsane Airdrop, suna nuna kamar an biya su 97.155 USDT a wallet. Misali:


Salisu D Crypto


Aminu Dayyib Zakariyya


Dukkaninsu sun ɗora screenshot iri ɗaya, wurin, lokaci, hash, wallet — duk daidai! 🤔

Wannan yana nuna cewa hoton ɗaya aka rarraba musu, ba gaskiya bane.


---


❌ Wannan Tsari SCAM ne!


Efsane Airdrop wani fake project ne da Reddit da masu bincike suka ce yana amfani da tactics kamar:


🔸 Fake payment proof

🔸 Referral yaudara

🔸 Phishing links da ke bukatar ka haɗa wallet


> A Reddit an ce:

“efsanetr.com is a scam collecting user data and selling it to the red market.”


---


🛡️ Yadda Zaka Kare Kanka:


1. Ka daina yarda da screenshot kawai — sukan kirkira ne ta Photoshop ko Canva.


2. Kada ka yarda da influencer kawai saboda suna da likes — wasu suna tallata scam domin suna biyan su.


3. Ka bincika project a CoinMarketCap, Reddit ko Twitter kafin shiga.


4. Use separate wallet don airdrops — kada ka haɗa main wallet ɗinka da dukiyarka.


5. Don’t give your private key or seed phrase!


---


🔚 Kar Ka Cika Wallet da Hasara


Abin da za ka rasa a fake airdrop ya fi girma fiye da abin da zaka samu.


> “Influencer na iya yarda da karyar da zai amfana da ita – kai fa?”


📢 Raba wannan post domin kare abokanka da danginka daga wannan fitina.


✍️ Nuhu Saad Kumurya

Post a Comment

Previous Post Next Post