Kada Ka Fada Tarkon Crypto: Muhimman Darussa Ga Sabbin Masu Shiga Duniya Crypto

 

Kada Ka Fada Tarkon Crypto: Muhimman Darussa Ga Sabbin Masu Shiga Duniya Crypto


Ita fa gaskiya biyuce da wadda kaji tayi maka daɗi da kuma wadda kaji bata yi maka daɗi ba ruwanka ne ka ɗauki wadda kake so.

Saide a mafi yawan lokuta wannan gaskiya wadda bama so itace daidai kuma mafita ga rayuwarmu.


Bari mu dawo gundarin maganar duk wanda yake cikin fagen Trading na Crypto kuma ya ɗauki koda shekara ɗayane ya san da cewa akwai dokoki wanda indai mutum ya karyasu abune me wahala bai jefa kansa cikin wahala ba.

Wannan kuwa itace :KADA KAYI CRYPTO DA KUƊIN ARO, AJIYA KO BUKATAR KUSA.

To amma suwaye suka fi karya wannan dokar? Mafi yawan wadanda suke karya wannan dokar sune wanda suke jin sun iya Crypton hakan yake basu ƙarfin gwuiwar amsar kudin mutane wanda daga ƙarshe kuma idan ba'a samu nasara ba sai Kaga mutum ya faɗa matsala wasu har abu yakai ga hukuma.

Tambayar anan shin ƙaddara ce ko ganganci?


Abu na gaba wannan ba shawara bace amma yana da kyau mutanenmu su lura dashi musamman wannan suke BEGINNERS ko FARIN SHIGA cikin duniyar mu sani 99.99% wanda ka gani a Crypto kuɗi suka zo nema wasu ido rufe wasu kuma ido buɗe kuma mafi akasarin kokarin gina hanyar samun kudinsu na farko suke shiyasa taimako yayi ƙaranci tsakanin yan Crypto. Domin irin taimakon da wasu suke nema kamar Kaine ka fara gini kaje linta sai wani yazo yace maka ka taimaka ka zaro bulo kamar kwas huɗu ka bashi zai fara nasa ginin ko kuma shima yana son yakai linta.

To kaga anan da yiyuwar ayi faɗuwar guzma..

Abun da ya dace da mutum shine idan kana son jin dadin Crypto a matakin farko ka tabbatar kana da hanyar samun kuɗi me gudana wadda kafi karfin abinci daga nan sai ka jajirce har ka samu wata kafa (Edge) a cikin Tsarin koda kana da niyyar rungumar Crypton gaba ɗaya.

Amma gangancine daukar Crypto 100% sana'a a karon farko ba tare da back up domin ita crypto har yanzu a bata tsaya da ƙafafunta ba 100%..


Daga ƙarshe kada haɗuwar social media tasa kaji haushin wani don ka nemi taimako daga wajensa yaƙi yi maka social media kaso me yawa packaging ne mutane da dama suna fama da rayuwa basu fito sun faɗa bane. A saboda haka wanda ya hanaka taimako baiyi laifi ba wanda ya taimaka maka sai ka gode masa domin shima baka san irin nasa matsalar ba..


Barkanmu da Sallah

Post a Comment

أحدث أقدم