Notification texts go here Contact Us Buy Now!

Isra’ila Ba Zata Iya Wannan Yaƙin Ba – Makaman Karya, Kuɗi Sun ƙare, Tsoro Ya Kama! 😅🔥🇮🇱



Isra'ila Ba Zata Iya Yaƙin Nan Ba, Lol 😀

Isra'ila tana kashe dala miliyan 285 a kullum a wannan yaƙin ta tsakanin su da iran.

Shafin jarida na Spectatorindex ya ruwaito cewa kasar Isra'ila tana kashe dala miliyan 285 a kowacce rana a wannan yaƙin da suke da Iran, wannan ya ƙara fito da raunin kasar Isra'ila a fili domin duk da uwar wadannan kuɗi da suke kashewa tare da makaman shingen su na Arrow-2, Arrow-3 da su Iron Dome da sauransu bai hana Iran dagargaza su ba tare da jefa masu manyan bamabamai a wurare masu mahimmanci na ƙasar, cikin harda hedkwatar cibiyar leƙen asiri ta ƙasar (Mossad), da tashar kasuwanci ta Haifa, wannan ya ƙara fito da zahirin tsaron su da suke yaɗa farfagandar cewa shi ne mai girma a duniya.

Daga ranar da aka fara wannan yaƙin Isra'ila ta shirya farfaganda iri-iri da sunan Amurka domin ta shigo da ita cikin yaƙin, wanda abinda yake ɓoye shi ne Isra'ila yakin nan ya fi ƙarfin ta, har ta kai a filin Tsinannen Firaministan su Netanyahu ya fara neman ɗauki kasashen duniya ciki harda Amurka da su shigo su tallafa masa a cikin yaƙi da Iran.

Kashe dala miliyan 285 a kullum, dai dai yake da kashe dala biliyan 104 a shekara idan yaƙin ya cigaba ya zama mai dogon zango. Iya kuɗin yaƙin nan kuwa sun ninka budget din tsaron Isra'ila sau 4 (dala biliyan 24 ~ SIPRI), makamin su na Iron Dome mai amfani da rokar Tamir da suka fi ji dashi a yana laƙume masu dala 40,000 a kowanne harsashin roka da zai harba, Iran na fatattakar su da daruruwan rokoki a kowace rana, saboda lissafin kuɗin su yana mugun haw-hawa, saboda yawan rokokin Tamir din da suke harbawa. Kuma Isra'ila ba tada karfin tattalin arzikin da zata ɗauki wannan kashe kuɗin yaƙin nan.

Ƙasar Amurka ita ce kasar da tafi turawa Isra'ila kuɗi a duk shekara, a ƙalla dala biliyan 3.3 duk shekara Amurka ke baiwa Isra'ila, dama masana suna cewa Isra'ila sune yan lelen Amurka da abinda Amurka da mallaka.

Tsohon mashawarci a fanni kuɗi ga Hukumar tsaron Isra'ila (IDF Financial adviser) Re’em Aminach ya ce Isra'ila na kashe dala miliyan 725 a kowacce rana a wannan yaƙin da suke da Iran, kimanin kashi 20 na gaba-daya tattalin arzikin ƙasar (GDP). Wanda wannan shi ne kididdiga mafi kusa da hakika musamman duba da wanda ya fadi maganar.

Isra'ila ba zata iya wannan yaƙin ba, makaman da suke karyar suna shi, sun gaza masu, kuɗin da suke kashewa sun yi yawa, basu da abinda zasu cigaba da ɗaukar dawainiyar wannan yaƙin shi yasa Netanyahu ya haukace da hauka iri-iri don yin duk abinda zai sanya Amurka ta kawo masa ɗauki ta shigar masa wannan yaƙi. Idan kuma ba haka ba to dole su rage ƙarfin abinda suka fito da shi filin daga, wannan kuma Nasara ce ga Iran domin zai bata damar ninka irin dagargazar da suke wa Isra'ila.

Ga rashin kuɗin cigaba da yaƙi, ga kuma rashin Nasara, wannan shi ne halin da Isra'ila take ciki.

Ya Allah ka cigaba da tabbatar da rashin Nasara ga ƙasa yahudawa, Isra'ila tare da ruguza duk mai taimakon Isra'ila. Amin.

Mustapha Alkasim Abubakar ✍🏼 
#gfatusupport4iran #israelisterroriststate

About the Author

Webmaster | Youtuber | Freelancer | Programmer | Sm Engineer | Blogger | Muslim | Sunni

Post a Comment

Cookie Consent
We serve cookies on this site to analyze traffic, remember your preferences, and optimize your experience.
Oops!
It seems there is something wrong with your internet connection. Please connect to the internet and start browsing again.
AdBlock Detected!
We have detected that you are using adblocking plugin in your browser.
The revenue we earn by the advertisements is used to manage this website, we request you to whitelist our website in your adblocking plugin.
Site is Blocked
Sorry! This site is not available in your country.