Naledi Pandor ta Karɓi Musulunci: Yadda Wasu Ke Gano Gaskiya, Wasu Kuma Suna Neman Bata ta
A kwanan nan na ga wata rubutu da ya ce fitacciyar ‘yar siyasar Afrika ta Kudu kuma babbar mai sukar Isra’ila, Naledi Pandor, ta karɓi Musulunci. A farko, sai na yi tunanin labari ne kawai maras tushe — fake news kenan. Amma daga bisani sai na tabbatar cewa gaskiya ne.
Wannan lamari ya ƙara mini tunani: Wasu da aka haifa cikin Musulunci suna zaginta, wasu kuma da ba a haife su a ciki ba suna ganinta a matsayin mafita kuma suna rungumarta da cikakken imani.
Shin wannan ba abin al’ajabi ba ne?
Na shafe shekaru ina rayuwa a ƙasashen yamma. A can na koyi girmama bambancin addini, ƙabila da ra’ayi. Amma abin mamaki ne yadda wasu daga cikin Hausawa ke kokarin wargaza addininsu da hannunsu.
Wasu daga cikinsu suna ɓoye ra’ayoyinsu a cikin rubuce-rubucensu. Idan ka karanta da hankali, za ka fahimci cewa ba su da niyyar gyara ko nasiha, illa dai su bata suna da raina addini. Wasu daga cikinsu ma suna jiran lokacin da za su fito fili su ce su ba Musulmi ba ne.
Gaskiya ne, kowa yana da 'yancin bin abin da ya ga dama. Amma abin takaici ne ganin yadda wasu ke wulakanta abin da wasu ke dauka da muhimmanci. Suna mai da raini da izgili tamkar wata hanya ce ta nuna wayewa ko ilimi — alhali kuwa wannan ba ilimi ba ne, karkacewa ce da girman kai.
A matsayinmu na Musulmi, mu da muka samu wannan ni’ima tun muna jarirai, bai kamata mu wulakanta ta ba. A maimakon hakan, mu gyara rayuwarmu, mu karantar da juna, mu kuma girmama addininmu da addinan wasu.
Allah ya shiryar da mu gaba ɗaya. Amin.
Rubutun: Muhsin
Post a Comment