Shugaban Najeriya Ya Bada Umarnin Daukar Ma'aikata 30,150 a Hukumi Biyar – Ga Yadda Zaka Nemi Aikin
Shugaban Najeriya Ya Bada Umarnin Daukar Ma'aikata 30,150 a Hukumi Biyar – Ga Yadda Zaka Nemi Aikin 🟣 Shugaban Najeriya Ya Amince da Daukar Ma’aikata Mutum 30,150 a Cikin 2025 A wani mataki na rage rashin aikin yi a Najeriya, gwamnatin tarayya ta amince da daukar sabbin ma’aikata har mutum 30,150 a wasu muhimman hukumomin gwamnati guda biyar. Wannan mataki zai kara damar samun aiki ga matasa da dama a fadin kasar. 🔰 Jerin Hukumomin da Za Su Dauki Ma'aikata ✅ 1. Nigerian Correctional Service (NCoS) Hukumar gyaran hali ta Najeriya za ta dauki mutum 5,150. Wannan hukumar na da alhakin kula da gidan yari da gyaran halin fursunoni. ✅ 2. Nigerian Immigration Service (NIS) Hukumar shige da fice za ta dauki mutum 10,000. Wannan dama ce ta musamman ga masu sha’awar aikin iyaka da kula da shige da fice. ✅ 3. Nigerian Security and Civil Defence Corps (NSCDC) Hukumar tsaro ta farin kaya zata dauki mutum 10,000. NSCDC na taka rawar gani wajen samar da tsaro a cikin gida da kiyaye kadarori...